NDLEA Tayi Abin da Ba a Taba Yi ba a Tsawon Shekara 33 a Karkashin Buba Marwa

NDLEA Tayi Abin da Ba a Taba Yi ba a Tsawon Shekara 33 a Karkashin Buba Marwa

  • Janar Buba Marwa ya yi bayanin nasarorin da Hukumar NDLEA ta samu a tsawon shekaru biyu
  • Shugaban na NDLEA ya ce a shekarar bara kurum, sun yi shari’a da mutum fiye da 2, 000 a kotu
  • Tsohon sojan ya gargadi masu harkar kwaya da suyi hattara domin za su kara yin tsauri a bana

Abuja - Shugaban NDLEA na kasa, Buba Marwa ya ce sun yi nasarar gurfanar da adadin mutanen da ya fi kowa yawa a tarihin kafuwar hukumar.

The Cable ta ce shugaban na NDLEA ya zanta da manema labarai a ranar Laraba 18 ga watan Junairu 2023, ganin ya cika shekaru biyu a bakin aiki.

A shekarar 2022 da ta wuce, Janar Buba Marwa mai ritaya ya ce hukumar NDLEA mai yaki da safarar miyagun kwayoyi ta kai mutane 2346 kotu.

Kara karanta wannan

Harkar Kwayoyi: Abin da Abba Kyari Ya Fada da aka Koma Sauraron Shari’arsa da NDLEA

Marwa ya gargadi ‘yan kwaya da iyayen gidansu su shirya domin a shekarar nan ta 2023, NDLEA za ta kara kaimi a wajen yakar miyagun kwayoyi.

Jawabin Janar Buba Marwa

"Yanzu haka mu na da manyan ‘yan kwaya 34 a hannunmu da ake shari’a da su a kotu. Mun yi nasar karbe kadarorinsu kafin a gama shari’a.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ganin yadda muke samun nasarori a kotu, sai su fara shiryawa rayuwa mai tsawo a gidan gyaran hali, kuma su sallama dukiyoyinsu har abada.
NDLEA
Shugaban kasa tare da Buba Marwa Hoto:newswirengr.com
Asali: UGC

A shekarun nan biyu (2021 da 2022), mun kama mutane 26, 458 masu safarar miyagun kwayoyi, daga cikinsu akwai manyan ‘yan kwaya 34."

- Buba Marwa

The Nation ta ce a shekarar bara kurum, NDLEA ta yi shari’a da mutane 2, 346 a gaban Alkali.

Kasashe ketare sun taimaka

Tun da aka kafa hukumar shekaru 33 da suka wuce, ba a taba yin lokacin da aka samu irin nasarar nan ba, akasari rabin wannan nasara ake yi.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Zan Warware Wasu Tsare-Tsaren El-Rufa'i Idan An Zabe Ni Gwamnan Kaduna, Uba Sani

Da yake jawabi, This Day ta rahoto Marwa yana godewa kasashen Amurka, Faransa, Jamus, Indiya, Koriya ta Arewa da Ingila a kan gudumuwarsu.

Abba Kyari va NDLEA

Ku na da labari da kotu ta zauna a ranar Laraba, Abba Kyari ya yi da’awar NDLEA ba ta da hurumin shari’a da shi, ya nemi ayi watsi da karar da ake yi.

Ana zargin ‘dan sandan da aka dakatar watau Abba Kyari tare da Sunday Ubia, Bawa James, Simon Agirigba, da kumaJohn Nuhu da harkar kwayoyi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel