An kama mutumin dake kai makamai Benue a Jigawa
Hukumar dake kula tare da hani ga ta’ammali da miyagun kwayoyi (NDLEA) a Jigawa ta kama wani mutumi da makamai a hanyarsa ta zuwa jihar Benue.
Mataimakin shugaban hukumar ta NDLEA a Jigawa, Oko Micheal ya bayyana hakan ga manema labarai a aranar Talata, 6 ga watan Fabrairu a garin Dutse, babban birnin jihar.
Mista Okoyace jami’an hukumar ta NDLEA na gudanar da ayyukansu kamar yadda suka saba a hanyar Jahun-Gujungu inda aka kama mai laifin.
A cewar hukumar, nan bada jimawa ba za a mika mai laifin da abubuwan da aka kwace zuwa hukumar yan sanda domin ci gaba da bincike.
KU KARANTA KUMA: Majalisa ta bukaci Malami da ya kare Metuh
Wanda ake zargin, Salisu Mahmouda, yace shi dan asalin jihar Kaduna ne. Yayi makaranta a Nasarawa inda daga baya ya shiga harkan kwasan karafuna tsakanin Nasarawa da jihar Benue.
Ya ce wasu yan kabilar Tiv guda biyu da Fulani ne suka bukaci ya kawo masu makamai, kuma sannan ya samu wanda yak era masa makaman a kauyen Labara dake Kano.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng