Tsugune Bata Kare Ba: Kungiyar TUC Ta Jero Sabbin Bukatu 10 Ga Tinubu, Ta Yi Gargadi Kan Aiwatarwa

Tsugune Bata Kare Ba: Kungiyar TUC Ta Jero Sabbin Bukatu 10 Ga Tinubu, Ta Yi Gargadi Kan Aiwatarwa

  • Yayin da ake sake shiga matsin tattalin arziki, kungiyar TUC ta tura bukatu ga Shugaba Tinubu
  • Kungiyar ta lissafo wasu sabbin bukatu 10 ga gwamnatin Shugaba Bola Tinubu yayin da aka shiga sabuwar shekara
  • Wannan na kunshe ne a cikin sanarwar da shugaban kungiyar, Festus Osifo da sakatarenta, Nuhu Toro suka sanya wa hannu

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Kungiyar Trade Union Congress (TUC) ta lissafo wasu sabbin bukatu 10 ga gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.

Kungiyar ta jero bukatun ne a cikin wata sanarwa da ta fitar ta sabuwar shekara don gaggawar kaddamar da su, BusinessDay ta tattaro.

Kara karanta wannan

"Abin da ke hana turawa suka dena shigowa yin kasuwanci a Najeriya", CNPP ta gargadi Tinubu

Kungiyar TUC ta lissafo manyan bukatu 10 ga Shugaba Tinubu
Kungiyar TUC lissafo sabbin bukatu 10 ga Tinubu. Hoto: @kc_journalist.
Asali: Twitter

Mene TUC ke bukata daga Tinubu?

Wannan na kunshe ne a cikin sanarwar da shugaban kungiyar, Festus Osifo da sakatarenta, Nuhu Toro suka sanya wa hannu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

The Nation ta tattaro cewa an fitar jerin sabbin bukatun ne a yau Alhamis 4 ga watan Janairu.

Kungiyar ta bukaci Shugaba Tinubu da ya tabbatar ya cika dukkan alkawuran da ya dauka tsakaninsa da Kungiyar Kwadago.

Sanarwar ta ce:

"Daga ciki akwai biyan naira dubu 30 na rage radadi ga ma'aikatan kananan hukumomi da jihohi da kuma Gwamnatin Tarayya.
"Kuma a tabbatar an kaddamar da wannan kafin bayyana sabon mafi karancin albashi a kasar."

Wasu bukatu TUC ta tura ga Tinubu?

Ga jerin bukatun guda 10:

1. Dole Gwamnatin Tarayya ta cika alkawarin mafi karancin albashi zuwa watan Afrilun 2024.

2. Dole ta biya dukkan basukan ma'aikata.

Kara karanta wannan

Gwamnan Arewa ya fadi babban burin Tinubu kan talakawan Najeriya, ya roki 'yan kasar kan hakuri

3. Dakile hauhawan farashin kaya da inganta tattalin arziki.

4. Ta rage yawan karbo basuka.

5. Dawo da martabar naira.

6. Siyarwa da kasuwancin naira a titunan Najeriya.

7. Rage farashin man fetur a kasar.

8. Hukunta jami'an gwamnati da ke ingiza rashin tsaro.

9. Samar da jami'an tsaron cikin al'umma.

10. Tattaunawa da dukkan kungiyoyi masu bukatu.

NLC ta gargadi Tinubu kan biyan dubu 35

A wani labarin, Kungiyar Kwadago ta NLC ta gargadi Shugaba Tinubu kan rashin biyan dubu 35 na rage radadi.

Wannan na zuwa ne bayan Gwamnatin ta dakatar da biyan kudaden bayan ta biya na wata daya kacal.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel