Matasan Yarbawa Sun Zakulo Minista, Sun Ayyana Shi Wanda Ya Fi Kowa Kokari

Matasan Yarbawa Sun Zakulo Minista, Sun Ayyana Shi Wanda Ya Fi Kowa Kokari

  • A duk ministocin da Bola Ahmed Tinubu ya nada, babu mai kokari kamar Muhammad Bello Matawalle
  • Wannan shi ne ra’ayin kungiyar matasan Kudu maso yamma wanda su ka jinjinawa karamin ministan tsaron
  • Kwamred Eric Oluwole yana so shugaba Bola Tinubu ya zabi Matawalle, ya ba shi lambar yabo na kwazonsa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - Matasa daga yankin Kudu maso yamma, sun ware Muhammad Bello Matawalle daga cikin sauran ministocin tarayya.

A yau This Day ta fitar da labari cewa karamin Ministan tsaron ya samu shaida mai kyau daga kungiyar matasan Kudu maso yamma.

Minista
Karamin Ministan tsaro, Bello Matawalle Hoto: Dr. Bello Matawalle/Olusegun Dada
Asali: Facebook

Matasa sun yabi Bello Matawalle a Ministoci

Kungiyar matasan da ke karkashin jagorancin Kwamred Eric Oluwole ta ce Muhammad Bello Matawalle ya cancanci yabo.

Kara karanta wannan

Hukumar EFCC ta kirkiri dakarun mutum 7,000 da za su yaki masu tashin farashin Dala

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ganin kokarin ministan musamman bayan ya je Saudiyya domin halartar taron ministocin tsaro na duniya ya jawo masa jinjina.

Matasan suna ganin Bello Matawalle ya taka rawar gani ta hanyar hada-kai da kasashen duniya domin tabbatar da zaman lafiya.

Minista: Kokarin Muhammad Bello Matawalle

A jawabin da Kwamred Eric Oluwole ya fitar, ya kara da cewa ba a dade da gama taro a Arewa ba, sai aka ga Matawalle a kasar Saudi.

Janar Abdulsalami Abubakar ya jagoranci zama a karshen watan Junairu da nufin kawo mafita a kan matsalar tsaron yankin Arewa.

"Matasan Yarbawa sun jinjinawa karamin Ministan tsaro, Bello Matawalle, musamman saboda yadda ya zo da karfinsa yana magance matsalolin tsaro a kasarmu.
Mu na so mu jinjinawa namijin kokarinsa a kan yadda yake bakin aiki, kuma ya sha alwashin barin ma'aikatar tsaron da kasa za tayi alfahari.

Kara karanta wannan

APC tayi maganar yunkurin dawo da Sanusi II gidan sarauta da rushe masarautun Kano

- Kwamred Eric Oluwole

Matawalle ya ba makiya kunya?

An rahoto kungiyar ta ce wannan kokari lamari ne da ba a saba gani a gwamnati ba.

A lokacin da aka nada Matawalle an yi ta surutu, amma kungiyar ta ce sa'ilin yana gwamna, ministan ya yi abin a yaba masa.

Oluwole a madadin matasan yankin na Kudu sun ce Bola Tinubu ya ayyana Ministan a matsayin wanda ya fi kowa kokari a ofis.

Ministan kudi ya ce an ceto tattali

Rahoto ya zo cewa Ministan tattalin arziki, Wale Edun ya yi ikirarin inda ake yanzu ta fuskar tattalin arzikin kasa ya fi inda aka baro.

In ban da an yi canjin gwamnati a ranar 29 ga watan Mayun 2023, Wale Edun yana ganin da Najeriya ta auka cikin masifar tattali.

Asali: Legit.ng

Online view pixel