Rayuwar Mahdi Shehu tana cikin garari, Iyalan babban dan kasuwa sun koka
- Iyalan Mahdi, wani babban dan kasuwan daga jihar Katsina, sun koka
- Sun ce rayuwarsa tana cikin hatsari saboda ba su ji daga gareshi
- A cewarsu, tun bayan 'yan sanda sun kama shi yake cikin mummunan yanayi
Iyalan wani babban dan kasuwa daga jihar Katsina, Mahdi Shehu, sun bayyana irin hatsarin da rayuwarsa take ciki, a ranar Talata, inda suka ce tun bayan 'yan sanda sun kama shi, ba su sake ji daga shi ba.
Tun bayan Mahdi Shehu, wanda shine shugaban Dialogue Groups, ya zargi gwamnatin jihar Katsina da yin almubazzaranci da naira biliyan 52.6 daga asusun tsaron jihar a shekaru 5 da suka gabata, ya shiga cikin tashin hankali.
Wani daga cikin iyalansa, ya tattauna da Daily Trust a ranar Talata, inda yace ranar karshe da suka ji daga gareshi shine bayan maciji ya sare shi a harabar hedkwatar 'yan sanda dake Area 10 a Garki, Abuja.
KU KARANTA: Ina cikin tashin hankali a jihata, kiranmu kadai ake da shugabannin tsaro, El-Rufai (Bidiyo)
"Ba mu da tabbacin ko yana da rai ko kuma ya mutu, saboda yanayin yadda 'yan sanda suke cutar da shi. Lafiyarshi ita ce babbar matsalar," cewar mutumin.
A makon da ya gabata, abokin Mahdi, Murtala Abubakar, ya tabbatar wa da Daily Trust cewa 'yan sanda sun kama shi.
An yi iyakar kokarin ganin an ji daga Hedkwatar 'yan sandan tun makon da ya gabata, amma abin ya ci tura. Har kokarin kira da tura sako ga kakakin hukumar 'yan sandan, Frank Mba aka yi a ranar Talata, amma bai amsa ba, kuma bai kira ba.
KU KARANTA: Rade-radin sabuwar zanga-zanga: FG ta sanar da tsatsauran matakin da za ta dauka
A wani labari na daban, labari da duminsa da ke zuwa daga jaridar HumAngle shine na sace jami'an gwamnatin jihar Borno da mayakan ta'addanci na ISWAP suka yi a ranar Litinin a Damasak.
Kamar yadda aka gano, jami'an gwamnatin suna tafiya ne a ababen hawa yayin da 'yan ta'addan suka tsare su a wani wuri da ake kira da Wakilti. Daga nan suka iza keyarsu tare da yin garkuwa da su domin neman kudin fansa.
Al'amuran ta'addanci yana cigaba da tsananta a yankin arewacin Najeriya, hakan kuwa yana ,matukar tada wa jama'a hankula tare da saka su yin kiraye-kiraye ga gwamnati da ta dauka mataki.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng