Yanzu nan: Hukumar DSS ta aikawa Alhaji Mahadi Shehu goron gayyata a Abuja

Yanzu nan: Hukumar DSS ta aikawa Alhaji Mahadi Shehu goron gayyata a Abuja

- DSS ta bukaci ganin Mahadi Shehu a babban ofishin ta da ke Abuja

- Kafin yanzu Attajirin ya fito ya yi wasu maganganu kan Gwamnati

- ‘Dan kasuwan ya ce zai amsa wannan goron gayyata da aka kai masa

Fitaccen ‘dan gwargwarmayar nan, kuma hamshakin ‘dan kasuwa, Alhaji Muhammad Mahdi Shehu, zai bayyana gaban hukumar DSS masu fararen kaya.

Jaridar Katsina Post ta fitar da rahoto a ranar Litinin 14 ga watan Satumba, 2020, cewa DSS ta bukaci ganin Muhammad Mahdi Shehu a farkon makon nan.

Ana zargin cewa gayyatar ba ta rasa alaka da maganganun da wannan Bawan Allah ya yi kwanakin baya inda ya ce Gwamnatin Katsina ta yi bindiga kudin tsaro.

KU KARANTA: Gwamnatin Katsina ta yi facaka da Biliyoyi daga 2015 zuwa yau

‘Dan kasuwan ya na zargin gwamnatin Aminu Bello Masari ta batar da abin da ya haura Naira biliyan 50 da sunan kudin tsaro a cikin shekaru biyar a Katsina.

Don haka ake sa ran Shehu zai bayyana a gaban babban ofisihin DSS da ke garin Abuja a yau.

Mahadi Shehu ya tabbatarwa ‘yan jarida cewa wannan goron gayyata ya shigo hannunsa, kuma ya ce zai amsa ta kamar yadda aka bukace shi a yau 14 ga Satumba.

Attajirin ya yi alkawarin zai yi magana da manema labarai game da yadda kayawarsu ta kasance da zarar ya fito daga hannun jami’an hukumar DSS na kasar.

KU KARANTA: Janar Tukur Buratai ya na barazanar maka Shehu a gaban kotu.

Mahadi Shehu ya tabbatar da wannan ne a lokacin da ya zanta da Katsina Post dazu ta sakon waya.

Yanzu nan: Hukumar DSS ta aikawa Alhaji Mahadi Shehu goron gayyata a Abuja

Gwamnan Katsina da Buhari Hoto: Fadar Shugaban kasa
Source: Twitter

Da aka nemi jin ta bakin Mahadi Shehu, ya bada tabbacin cewa sakon gayyatar DSS ya shigo hannunsa. Ya ce amma bai da masaniyar abin da ya sa ake nemansa.

Shehu ya ce: “Eh, an gayyace ni, amma ban san dalilin ba.”

“Zan amsa kiran da aka yi mani, kuma zan sanar da ‘yan jarida duk abin da ya faru daga baya.”

“Nagode.” Inji ‘Dan kasuwan.

Da ya ke bankado wasu zargi a baya, Mahadi Shehu ya ce ya kamata gwamnan Katsina Aminu Masari ya yi murabus saboda irin badakalar da ake zarginsa da aikatawa.

A na ta bangaren, gwamnatin Katsina ta karyata wadannan zargi da 'dan kasuwan ya jefa mata. Wannan raddi ya fito ne ta bakin sakataren gwamnatin jihar, Mustafa Inuwa.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit Nigeria

Online view pixel