Tashin Hankali Yayin da Gobara Ta Kashe Yaro Dan Shekara 4 a Jihar Kano

Tashin Hankali Yayin da Gobara Ta Kashe Yaro Dan Shekara 4 a Jihar Kano

  • Hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta tabbatar da cewa wata gobara ta lakume rayuwar wani yaro dan shekara 4 a unguwar Yakasai
  • Kakakin hukumar, Saminu Abdullahi ya ruwaito cewa karamin yaron na wasa da ashana, lokacin da wuta ta kyastu tare da haddasa gobarar
  • Duk da cewa an ceto yaron daga ginin da gobarar ta kama, sai dai likitoci a asibitin Murtala sun tabbatar da mutuwarsa

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Kano - Wata gobara ta salwantar da rayuwar wani yaro dan shekara 4 mai suna Abubakar Sani, wanda aka fi sani da Musaddiq a unguwar Yakasai da ke birnin Kano.

Jami’in hulda da jama’a na hukumar kashe gobara ta jihar Saminu Yusif Abudullahi ya tabbatar da faruwar lamarin, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Kogi: Yan bindiga sun sace fasinjojin wasu manyan motoci guda biyu a hanyar zuwa Abuja

Gobara ta tashi sanadin wasa da ashana, karamin yaro ya mutu a Kano
Gobara ta tashi sanadin wasa da ashana, karamin yaro ya mutu a Kano Hoto: @Fedfireng
Asali: Facebook

An gano abin da ya haddasa gobarar

Mista Abudullahi ya ce gobarar ta rutsa da yaron a cikin daki amma daga baya aka ceto shi a sume, inda aka tabbatar da mutuwarsa a asibitin Murtala Muhammad.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce:

“An gano yaron ne a wani gini mai hawa daya mai kimanin kafa 40 x 30, bayan da wuta ta kama wani daki a sama tare da tsallakawa zuwa falo.
“An mika gawar yaron ga mahaifinsa, Sani Usaini a asibiti domin yi masa jana’iza kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.”

Ya kuma tabbatar da cewa gobarar ta tashi ne sakamakon yadda wanda abin ya rutsa da shi ke wasa da ashana a cikin daki, lamarin da ya ja gobarar ta kama ginin.

Dalilin da yasa darajar Naira ke faduwa

Babban bankin Najeriya (CBN) ya ce ya gano wani babban dalili da ya sa darajar Naira ke ci gaba da faduwa a kasuwar hada-hadar kudi ta duniya.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Katsina ta dauki gagarumin mataki bayan 'yan bindiga sun kwashe 'yan kai amarya 60

Gwamnan CBN, Yemi Cardoso ya ce sun gudanar da wani bincike da ya nuna cewa akwai kudin da suka kai dala biliyan 2.4 da ake hankoron Najeriya ta gaza biya kuma na boge ne.

Ya ce har zuwa lokacin da aka kammala bincike babu wani mai saka hannun jari da ya nuna cewa kudin hakkin sa ne, don haka bankin ke zargin an kitsa maganar ne don a karya darajar Naira.

Asali: Legit.ng

Online view pixel