Jagora a APC Ya Shaidawa Tinubu Abin da Ake Bukata da Gaggawa Domin Zaman Lafiya

Jagora a APC Ya Shaidawa Tinubu Abin da Ake Bukata da Gaggawa Domin Zaman Lafiya

  • Gbenga Olawepo-Hashim ya fitar da jawabi inda ya jaddada kiran kafa ‘yan sanda a matakin jihohin kasa
  • ‘Dan takaran shugaban kasar yana so gwamnatin Bola Tinubu tayi wa tsarin mulki kwaskwarima
  • Tunanin da Olawepo-Hashim yake yi shi ne idan kowace jiha ta mallaki ‘yan sanda, za a samu sauki

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Kwara - Gbenga Olawepo-Hashim wanda ya taba neman takarar shugaban kasa, ya fito yana mai kira ga Bola Ahmed Tinubu.

The Guardian ta fitar da labari cewa Gbenga Olawepo-Hashim ya nemi gwamnatin Najeriya ta samar da ‘yan sandan jihohi.

Bola Tinubu
Ana so Bola Tinubu ya kawo tsaro Hoto: Buhari Sallau
Asali: Facebook

Ganin yadda aka kashe Mai martaba Janar Oba Olusegun Aremu, ‘dan siyasar ya kawo shawarar yadda za a iya samar da tsaro.

Kara karanta wannan

Buhari ne sanadi: Jagora a APC ya fadi wanda ya jefa tattalin Najeriya a mawuyacin hali

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Idan ana so matsalar rashin tsaro ta zama tsohon labari, Gbenga Olawepo-Hashim ya ce dole a rage dogaro da ‘yan sanda na tarayya.

Olawepo-Hashim ya yi magana jiya a garin Ilorin da ke jihar Kwara, inda ya soki kashe-kashen da aka yi a ‘yan kwanakin nan.

Bola Tinubu yana bata lokaci

‘Dan takaran shugabancin kasar ya ce bai ga dalilin Bola Tinubu na bata lokaci a wajen kawo sauyi a kan sha’anin ‘yan sanda ba.

Tun da APC ta ke rike da jihohi da yawa da rinjaye a majalisu, Olawepo-Hashim yana so a samar da ‘yan sanda dabam da na tarayya.

'Yan sandan jihohi za su magance komai?

Tribune ta rahoto ‘dan siyasar yana cewa kafa ‘yan sanda a jihohi ba zai yaye daukacin matsalar ba, amma za a magance rabi.

Kara karanta wannan

Mai ba Jonathan shawara ya nunawa Tinubu hanyar farfado darajar Naira kan Dala

Shi Olawepo-Hashim yana ganin a mako guda za a iya gama tsara yadda jihohi za su kafa ‘yan sandansu ta hannun majalisun dokoki.

A jawabinsa, ya yi kira ga gwamnatin Bola Tinubu ta tashi tsaye a daina kashe al’umma da garkuwa da mutane a fadin kasar nan.

Jigon na APC ya ce wannan kira ya ci karo da sashe na 214 na kundin tsarin mulki, amma tabarbarewar tsaro ya jawo ake neman sauyi.

Kashe-kashe a gwamnatin APC

Ana da labari cewa an rasa dubunnan rayuka kuma an yi garkuwa da mutane sama da 17, 000 tsakanin 2019 zuwa yau a jihohin Najeriya.

Duk da an ci karfin Boko Haram, an fuskanci barazanar tsaro a zamanin Muhammadu Buhari da magajinsa watau Bola Tinubu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng