Ni zan yi nasara kan Buhari da Atiku a zaben 2019 - Olawepo Hashim
A yayin da guguwar siyasa ta yi kane-kane a duk wasu lunguna da sakonni na kasar nan, a jiya Litinin wani sabon dan takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar Peoples Trust PT, ya sha alwashin lallasa shugaban kasa Muhammadu Buhari da kuma tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar a yayin babban zabe na 2019.
Da yake gabatar da jawabansa yin zaman sauraron ra'ayin al'umma da aka gudanar cikin birnin Abuja, Mista Gbenga Olawepo-Hashim, ya shaidawa magoya bayan sa cewa tuni ya kammala duk wani shiri na tabbatar da wannan kudiri da ya sanya a gaba.
Kamar yadda shafin jaridar The Nation ya ruwaito, Mista Gbenga ya bayyana cewa 'yan siyasar kasar nan za su sha mamakin yadda za a samu wani sauyi na juyin juya hali ta fuskar kada kuri'u cikin akwatunan zabe a badi.
Yake cewa, lokaci ya kawo da ya kamata ayi watsi da tsoffafin 'yan siyasa da suka dade su na damawa kan madafun iko na kasar nan musamman yadda mutane 'yan kalilan ke ribatar da samun dama ta tsose romon gwamnatin Najeriya.
Olawepo ya ci gaba da cewa, zaben 2019 na badi lokaci da al'ummar kasar nan za ta kawo karshen kisan kiyashi, wahalhalu na rayuwa da kuma matsananciyar yunwa da ta yi zaman dirshan a sanadiyar rikon sakainar kashi na jagorori da masu rike da madafun iko a kasar nan.
A yayin daya ke ci gaba da kalubalantar gazawar gwamnatin kasar nan ta fuskar rashin hangen nesa, rashin kyawawan tsare-tsare da za su fidda Najeriya zuwa ga tudun tsira, Mista Gbenga ya sha alwashin biyan N50, 000 a matsayin mafi karancin albashin ma'aikata yayin bikin murnar cikarsa shekara guda a kan karagar mulki ta kasar nan.
KARANTA KUMA: Buhari ya gaza ladabtar da El-Rufa'i - Shehu Sani
Jaridar Legit.ng ta fahimci cewa, Mista Gbenga yayin yiwa gwamnatin kasar nan wankin babban Bargo, ya kuma kaddamar da cewa jam'iyyar PT ita kadai ce zabin al'ummar kasar nan yayin babban zabe na 2019 da za ta fidda A'i daga Rogo.
Kazalika jaridar ta Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, shugaban jam'iyyar APC na kasa Kwamared Adams Oshiomhole, ya yi zargin cewa ana yiwa mambobin jam'iyyarsa kisan mummuke a jihohin da jam'iyyar adawa ta PDP ke mulki a fadin kasar nan.
Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:
https://facebook.com/legitnghausa
https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng