Bayan shan kashi a takarar Shugaban kasa, Olawepo-Hashim ya bi Buhari zuwa APC

Bayan shan kashi a takarar Shugaban kasa, Olawepo-Hashim ya bi Buhari zuwa APC

  • Gbenga Olawepo-Hashim ya bada sanarwar koma wa jam’iyyar APC mai mulki
  • Olawepo-Hashim ya nemi kujerar shugaban kasa karkashin jam’iyyar PT a 2019
  • ‘Dan siyasar ya bayyana dalilinsa na shiga APC da wadanda suka karfafa masa

Abuja - ‘Dan takarar kujerar shugaban kasa a zaben 2019, Gbenga Olawepo-Hashim, ya bada sanarwar fice wa daga jam’iyyar PT, ya koma APC mai mulki.

Buhari ya sa Gbenga Olawepo-Hashim ya bi APC

Punch ta ce Gbenga Olawepo-Hashim ya bada wannan sanarwa a wani jawabi da ya fitar ga manema labarai a Abuja a ranar Laraba, 4 ga watan Agusta, 2021.

Olawepo-Hashim yace ya zabi APC ne saboda jam’iyyar ce za ta iya hada-kai da kawo cigaba a kasar nan.

A jawabin na sa, Olawepo-Hashim ya bayyana cewa ya gamsu cewa shugaan kasa Muhammadu Buhari da gaske yake yi wajen yaki da rashin gaskiya a Najeriya.

Olawepo-Hashim ya zauna da jiga-jigan APC

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: PDP ta saki bidiyo, ta yanke muhimmiyar shawara

Tuni dai Olawepo-Hashim ya yi rajista a mazabarsa da ke Usuma a birnin tarayya Abuja. Hashim ya tuntubi manyan ‘yan siyasa kafin ya koma jam’iyyar ta APC.

Kafin ya dauki wannan mataki, sai da tsohon ‘dan takarar shugaban kasar ya zauna da gwamnan jihar Kwara, Abdulrahman Abdulrazak da Sanata Geoge Akume.

Olawepo-Hashim
Olawepo-Hashim Hoto: www.tribuneonlineng.com
Asali: UGC

A cewarsa, tun bayan zaben 2019 ya gane cewa akwai bukatar ya bi jirgin daya daga cikin manyan jam’iyyun da ake da su, domin tafiyar siyasarsa ta samu karbu wa.

“A watanni shidan da suka wuce, na zauna da shugaban rikon kwarya na APC, Mai Mala Buni sau biyu da ‘danuwana, abokina, AGF, Abubakar Malami (SAN).
“Baya ga taron da mu ka yi da Ministan birnin tarayya Abuja, Mustapha Bello, wanda shi ne shugaban APC a Abuja, kuma yana cikin majalisar zartar wa.”

Jaridar Sun ta ce fitaccen ‘dan kasuwan ya sa hannu da kansa a wannan jawabi da aka fitar dazu. 'Dan siyasar bai kai labari da ya nemi takara a zaben da ya wuce ba.

Kara karanta wannan

A karshe tsohon Shugaban INEC ya yi watsi da APC da PDP, ya shiga PRP, ya bayyana dalilai

Ana fama da rikicin cikin gida a PDP

A daidai wannan lokaci, rikicin cikin gida ya na neman ya ci jam'iyyar adawa ta PDP: Wasu gwamnonin jihohi su na so su yi waje da shugabannin jam'iyyar na kasa.

Rahotanni sun bayyana cewa Gwamnan Ribas, Nyesom Wike ya hada-kai da takwarorinsa, sun huro wa Prince Uche Secondus da sauran shugabannin jam’iyyar wuta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng