An Cafke Makiyayan da Suka Kashe Fitaccen Malamin Addini a Wata Jihar PDP

An Cafke Makiyayan da Suka Kashe Fitaccen Malamin Addini a Wata Jihar PDP

  • An kama wasu makiyaya uku da ake zargi da kisan wani fasto a yankin Gege da ke Igbomoso, jihar Oyo
  • An kashe malamin addinin, Fasto Segun Adegboyega yayin da yake kalubalantar makiyayan da suka farmaki gonarsa da dabbobinsu
  • Mazauna kauyen ne suka kama makiyayan sannan aka mika su hedkwatar rundunar 'yan sanda ta Owode don gudanar da bincike

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Jihar Oyo - An kama wasu makiyaya uku da ake zargin suna da hannu a kisan wani fasto a yankin Ogbomoso, jihar Oyo.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa wasu mahara da ake zaton makiyaya ne sun kashe Fasto Adegboyega a garin Ogbomoso.

An kama makiyaya kan kisan malamin addini
An Cafke Makiyayan da Suka Kashe Fitaccen Malamin Addini a Wata Jihar PDP Hoto: Nigeria Police Force
Asali: Facebook

An tattaro cewa an kashe marigayin ne a yankin Gege da ke hanyar Ogbomoso-Iseyin lokacin da ya kalubalanci makiyayan, wadanda suka farmaki gonarsa da dabbobinsu domin su yi kiwo da amfanin gonarsa.

Kara karanta wannan

Miyagun 'yan bindiga sun kai ƙazamin hari, sun halaka ƴan sanda da wasu bayin Allah a jihar APC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jaridar ta kuma rahoto cewa mazauna kauyen ne suka kama makiyayan su uku sannan nan take suka kai su fadar sarkin Ogomosho, Oba Afolabi Ghandi Olaoye.

Daga nan sai aka mika wadanda ake zargin hannun 'yan sanda domin gudanar da bincike.

An ajiye gawar mamacin a wani dakin ajiyan gawa mai zaman kansa.

Sarkin Ogbomoso ya yi kira ga talakawansa

A halin da ake ciki, Oba Olaoye ya roki jama'a da su kwantar da hankalinsu kan lamarin, jaridar Punch ta ruwaito.

Basaraken ya yi alkawarin aiki tare da jami’an tsaro domin nemawa iyalan marigayin adalci.

Basaraken ya ce:

“A matsayina na mahaifinku, ina so in ce, wannan mummunan yanayi ne kuma abu ne da ba za a yarda da shi ba.
"Na fada ma kwamandan ‘yan sanda na yankin Owode zuciyata, wanda ya kasance tare da ni anan kuma ina so in tabbatar muku da cewa za a yi adalci.

Kara karanta wannan

Kalaman Buhari sun jawo za a binciki inda Gwamnoni 150 da Ministoci Suka Kai N40tr

"Ina kuma jajanta wa kowa da kowa, da fatan Allah Ya ci gaba da kula da ku da daukacin kasar Ogbomoso.”

'Yan bindiga sun sace dalibai

A wani labarin, wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun yi awon gaba da wasu yara ‘yan makaranta da ba a tantance adadinsu ba a karamar hukumar Emure da ke jihar Ekiti a yammacin jiya.

Duk da cewa har yanzu ba a samu cikakken bayani kan harin ba, kuma ba a bayyana sunan makarantar da aka sace wa daliban ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel