Gwamnati Za Ta Yaki Masu Saba Doka, Minista Ya Umarci a Cafke Mutane a Manyan Titi

Gwamnati Za Ta Yaki Masu Saba Doka, Minista Ya Umarci a Cafke Mutane a Manyan Titi

  • David Umahi ya je jihar Abia domin ganin inda aka kwana a aikin hanyar Aba – Enugu – Fatakwal
  • A garin Aba ne Ministan ayyukan ya ci karo da wadanda suke kasuwanci a titin da ake kokarin ginawa
  • Sanata Umahi ya bada umarnin kamo masu wannan danyen aiki, ya sha alwashin zai kai su kotu

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abja - Ministan ayyuka ya bada umarnin cafke wasu mutane da ke talla a kan hanyar Enugu zuwa Fatakwal da ake gyarawa.

Jaridar Premium Times tana cikin wadanda suka fitar da labarin nan a karshen makon jiya.

Minista
Ministan ayyuka a ofis Hoto: @realdaveumahi
Asali: Twitter

Ziyarar Ministan ayyuka zuwa Aba

A ranar Asabar David Umahi ya bada wannan umarni yayin da ziyarci garin Abia domin ganin yadda aikin babban titin yake tafiya.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun kwamushe mutum 10 da ake zargin masu garkuwa da mutane ne a jihar Akwa Ibom

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanata David Umahi bai ji dadin yadda wasu suke kasuwanci a bangaren garin Aba na wannan hanya da ta ratsa jihohin kudu da-dama.

A yayin da ya ci karo da wasu suna talla a titin, mai girma Ministan ya bukaci wasu cikin jami’an tsaron da ke gadinsa su cafke masu su.

Minista zai kai 'yan talla kotu

Wannan lamari ya fusata ministan ayyukan, ya tabbatar da cewa za a gurfanar da ‘yan kasuwan a kotu domin doka ta hukunta su.

Ministan ya zargi masu kasuwancin da saba doka, jefa kan su a hadari da hana ‘yan kwangila yin aiki baya ga jawo kazanta.

"Da alama wasu a nan suna so su ji wa kansu ciwo ne da kan su. Ba za mu su iya barin ‘yan kwangila suyi aiki ba."
"Suna sabawa dokokin titi. Suna amfani da titunan da aka gama a matsayin wurin ajiye motoci, kasuwanci da zubar da shara."

Kara karanta wannan

Dubu ta cika: An kama wani mai yin sojan gona a matsayin kakakin majalisar dokokin jihar arewa

"Kusan gaba daya bolar Aba ake jibgewa a titin nan. Sam wannan bai dace ba."
"Zan ba gwamnati shawara ta kafa jami’an tabbatar da doka a nan."

- David Umahi

Umahi yace ba za ta yiwu ba

Vanguard ta rahoto Umahi yana cewa ba za ta yiwu gwamnatin tarayya ta kashe kudi wajen gina tituna, wasu mutane su rika gine-gine a kai ba.

Idan ana so a kammala aikin babban titin, dole a bar ‘yan kwangila su zage suyi aikinsu.

Kungiyar SERAP da Gwamnoni

Gwamnoni kimanin 150 da manyan Ministocin Abuja takwas aka yi daga 1999 zuwa shekarar nan, ana da labari SERAP ta taso su a gaba.

SERAP tana zargin Gwamnonin jihohi suna lakume kudin da aka warewa kananan hukumominsu, don haka suke barazanar zuwa kotu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel