Dubu Ta Cika: An Kama Wani Mai Yin Sojan Gona a Matsayin Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Arewa

Dubu Ta Cika: An Kama Wani Mai Yin Sojan Gona a Matsayin Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Arewa

  • Ƴan sanda sun kama wani da ake zargi da yin sojan gona da sunan shugaban majalisar dokokin jihar Jigawa
  • Kwamishinan ƴan sanda, Ahmadu Abdullahi, ya ce yayin bincike sun gano katunan shaida masu ɗauke da bayanan kakakin
  • Jami'an tsaron sun kuma damke wani matashi da ake zargi da safarar miyagun kwayoyi a tashar motar Babura

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jigawa - Rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa ta kama wani mutum mai shekaru 39 da laifin nuna kansa a matsayin shugaban majalisar dokokin jihar, Alhaji Aliyu Haruna.

Kwamishinan ƴan sandan jihar, CP Ahmadu Abdullahi, ne ya bayyana haka yayin hira da manema labarai, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Kano: Kotu ta dauki mummunan mataki kan 'yan bijilanti 5 saboda dalili 1 tak, sun yi martani

Yan sanda sun kama sojan gona a Jigawa.
Yan sanda sun kama wanda ake zargi da yin sojan gonar kakakin majalisar Jigawa Hoto: PoliceNG
Asali: Twitter

CP ya ce wanda ake zargi da yin sojan gonar mai suna, Abduljabar Inuwa, mazaunin anguwar Zai a Dutse, ya shiga hannun jami'an ƴan sanda ranar Litinin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya bayyana cewa an kama wanda ake zargin ne a lokacin da yake rike da katin shaida na jabu masu dauke da suna da alamar kakakin majalisar dokokin jihar Jigawa.

Kwamishinan ya kara da cewa, a lokacin da aka gudanar da bincike a gidan wanda ake zargin, an samu karin wasu katunan na bogi guda 20.

A cewarsa, wanda ake zargin ya amsa laifin cewa ya samu kudade daga shugabannin ƙananan hukumomin jihar da sunan shugaban majalisar.

CP Abdullahi ya kara da cewa an kama wani mutum da ya buga katunan kyauta ga wanda ake zargin, The Angle ta tattaro.

Ƴan sanda sun kama karin masu laifi

Kara karanta wannan

Yan sanda sun ki karbar cin hancin naira miliyan 1, sun kama dan bindiga a otal din Kaduna

Kwamishinan ya ce sun kuma kama wani matashi dan shekara 25, Abdullahi Suleiman, da ke zaune a unguwar Kanti a Kazaure da laifin lalata igiyoyin wutar lantarki a unguwar.

“Wani mai suna Abdullahi Isa da ke wannan adireshin ya koka cewa ya gano wanda ake zargin a lokacin da yake aikata laifin, kuma da ya tambaye shi, wanda ake zargin ya kai masa hari tare da daba masa wuka."

Ya kuma ce ‘yan sandan sun kama wani matashi dan shekara 25 mai suna Yusif Musa da ke unguwar Kafar Yamma, Babura, wanda ake zargi da safarar miyagun kwayoyi a tashar mota ta Babura.

Ƴan bindiga sun yi garkuwa da DVC

A wani rahoton na daban Ƴan bindiga sun yi garkuwa da mataimakin shugaban jami'ar ABSU, DVC Farfesa Godwin Emezue a jihar Abiya.

Ganau sun bayyana cewa maharan sun tare Farfesan ne a gidan mai yayin da ya je shan mai a motarsa, suka tafi da shi zuwa inda ba a sani ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel