“Hajiyar Suwaga”: Mercy Aigbe Ta Tashi Kan Masoya, Ta Saki Zafafan Hotunanta Tare Da Mijinta a Hajji

“Hajiyar Suwaga”: Mercy Aigbe Ta Tashi Kan Masoya, Ta Saki Zafafan Hotunanta Tare Da Mijinta a Hajji

  • Jarumar Nollywood Mercy Aigbe da mijinta Kazem Adeoti, wanda aka fi sani da Adekaz suna kasar Saudiyya domin sauke farali
  • Matar wacce ke da yara biyu ta wallafa hotunan da suka dauka tare da mijinta sanye da harami domin aikin hajji
  • Masoya da abokan sana'ar jarumar sun garzaya sashin sharhi domin yaba kyawun da suka yi tare da mijinta

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Mercy Aigbe na daya daga cikin yan tsirarun jarumai da suke sauke farali a garin Makkah, kuma tana ta baiwa masoyanta karin bayani kan yadda abubuwa ke gudana.

Jarumar ta yi sabon wallafa a shafinta, tana mai nunawa duniya mijinta a hotuna daban-daban.

Mercy Aigbe da mijinta
“Hajiyar Suwaga”: Mercy Aigbe Ta Tashi Kan Masoya, Ta Saki Zafafan Hotunanta Tare Da Mijinta a Hajji Hoto: @realmercyaigbe
Asali: Instagram

Kamar yadda ake bukata daga kowani mahajjaci, ma'auratan sun kasance sanye da harami inda Mercy ke sanye da hijabi dogo da tsadadiyar jakarta ta hannu da gilashin ido.

Kara karanta wannan

Innalillahi: 'Yan Ta'adda Sun Kashe Basarake Bisa Kuskure, Sun Sace Mutum 3 a Wata Jihar Arewa

A wallafarta, matashiyar ta bayyana cewa bata da abun da za ta ce sai dai godiya ga Allah.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ta rubuta:

"Babu abun cewa sai Alhamdulilah."

Kalli wallafar a kasa:

Jama'a sun yi martani

Masoyanta musulmai sun nuna farin ciki ganin cewa jarumar ta karbi Musulunci a karshe.

Karanta wasu daga cikin martanin a kasa:

fowobihichart:

"Kina sa Musulunci ya kara kyau."

gleeoflife:

"Hajiyar ado."

folagade_banks:

"Kyakkyawa ❤️"

queen_olatikitan19:

"Idan da kyau mutum ne."

baliqees360:

"@realmercy kin ga cewa musulunci na da kyau ko."

horllannikky:

"Allihamdulilah! Awww! Wannan ya yi kyau."

kitchen_essentials.ng:

"Hadaddun mutane."

bola2.324:

"Kyakkyawar Hajia Minah."

amalbotanicals:

"Muna so maki wannan."

folex_exclusives:

"Fada mani me ya fi wannan kyau...Karin so."

hind_procurement_brand:

"Kyawu tsantsa♥️ ❤️❤️ kina lafiya hajiya."

Kara karanta wannan

“Ta Tsere”: Matar Aure Ta Yashe Gaba Daya Asusun Bankin Da Suke Tara Kudi Da Mijinta, Ta Yi Batan Dabo

cuteloveroflove:

"Alhaji da Hajia Adeoti ❤️"

Daga Karshe Jarumar Fim, Mercy Aigbe Ta Tabbatar Da Shiga Musulunci

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Mercy Aigbe ta sa masu amfani da soshiyal midiya yamutsa gashin baki bayan bayyanan wani bidiyonta da ya yadu.

Ku tuna cewa jarumar da mijinta, Adekaz sun gayyaci abokai, abokan sana'a da yan uwa zuwa taron Ramadan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel