Malamin Makarantar Islamiyya Ya Shiga Babbar Matsala Bayan Ya Lakadawa Karamin Yaro Dukan Tsiya
- Wani malamin makarantar Islamiyya ya jefa kansa a matsala bayan da ya lakadawa karamin yaro dukan tsiya saboda ya gaza yin karatu
- Hukumar kare hakkin kananan yara ta jihar Neja ce ta shigar da korafin gaban ofishin 'yan sanda da ke Minna, kuma an kama malamin
- Legit Hausa ta tattauna da wani shugaban makarantar Islamiyya kan matakin da aka dauka akan malamin da ya lakadawa dalibin dukan tsiya
Sani Hamza, kwararren edita ne a fanni n nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Jihar Neja - A garin Suleja ne, jihar Neja, aka samu wani malamin makarantar Islamiyya mai suna Mallam Nura, ya lakadawa dalibinsa dukan tsiya har ta kai ga ya farfasa masa jiki.
Rundunar 'yan sandan Minna sun kama malamin bayan da hukumar kare hakkin kananan yara ta jihar Neja ta shigar da korafi akan sa.
Daga jihar Kaduna aka kai Mu'azu karatu Neja
An ruwaito cewa malamin ya zane dalibin mai suna Isah Mu'azu, dan shekara 11 saboda ya gaza haddace wani sashe na Al-Kur'ani da ya umurce shi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Haka zalika an gano cewa iyayen Mu'azu na zaune ne a yankin Kawo da ke jihar Kaduna, sun kai shi Neja ne domin yayi karatun Al-Kur'ani tare da dan uwansa.
Mukaddashin daraktan hukumar kare hakkin kananan yara ta jihar, Suleiman Shehu ya shaidawa Daily Trust cewa an kama malamin tare da mika sa ga 'yan sanda.
Aikin hukumar NSCRA a jihar Neja
Shehu ya kuma ce sun gayyaci mahaifin yaron zuwa Minna yayin da sashen CID na garin za su tuhumi malamin.
Sannan ya ce an kai yaron zuwa asibiti domin yi masa magani, inda ya kara da cewa za a gurfanar da mai laifin gaban kotu da zaran an gama bincike.
Me ya sa aka raina malaman makarantun addini?
Wani shugaban makarantar Islamiyya a garin Funtua, jihar Katsina, Mallam Abdulrahman ya ce iyaye da ma wasu hukumomi sun raina malaman addini akan na boko.
Mallam Abdulrahman na yin martani ne kan kama malamin Islamiyya da aka yi a Neja saboda ta doki dalibinsa.
A zantawarsa da Legit Hausa, Mallam Abdulrahman ya ce:
"Sam bana goyon bayan a rinka yi wa yara dukan da ya wuce hankali, don hakan yana kangarar da su maimakon horas da su, sai dai kuma an raina malaman addini da yawa.
"Idan da za ka je makarantun kwana, har ma da na je ka ka dawo, ka ga irin dukan da ake yi wa dalibai sai ka yi mamaki, kuma iyaye ba sa cewa komai akai.
"Amma nan Islamiyya, karamin duka za a yi wa dalibi zai sanar da iyayen sa, su zo har makaranta su ci mutuncin malamai. Shi ya sa daliban ba sa ganin girman malamansu."
Mallam Abdulrahman ya shawarci malaman makarantun Islamiyya da su rinka yin amfani da wani nauyin hukunci ga dalibai maimakon dukan da ya wuce tunani.
Ya kuma yi kira ga gwamnatin jihar Neja da ta sassauta wa malamin da aka kama, yana mai cewa, ana hukunta yaro ne don a gyara tarbiyyar sa.
Kada sun yi kalaci da fasto a rafi yayin bikin baftisma
A wani labarin kuma,wasu gungun kadoji sun yi karin kumallo da wani fasto a rafin Olifants da ke Limpopo, yayin bikin baftisma
An ruwaito cewa faston da abokan aikinsa biyu ne suka shiga rafin, amma shi kadai kadojin suka farmaka, kuma har yanzu an gaza tsamo abin da ya yi saura daga sassan jikinsa.
Asali: Legit.ng