Kada Sunyi Kalace da Fasto a Rafi Yayin Bikin Baftisma

Kada Sunyi Kalace da Fasto a Rafi Yayin Bikin Baftisma

  • A wani abu mai ban al'ajabi da tausayi, gungun kadoji sun yi kalaci da wani fasto da ya shiga rafi da wasu mutum biyu yin baftisma
  • Rahotanni sun bayyana cewa kadojin sun yi fata-fata da naman shi, wanda aka gano a rafin Olifants da ke Limpopo, Afrika ta Kudu
  • Yan sanda a kasar sun gargadi mutane da su guji shiga rafukan da suka san akwai kadoji a ciki don gudun zama kalacin 'yan ruwan

Sani Hamza, kwararren edita ne a fanni n nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Afrika ta Kudu - Wani mutum da ya yi iƙirarin cewa shi ma'aiki ne, ya nutse cikin ruwa kuma nan take kada suka yi kaca-kaca da naman shi a lokacin da ake yin baftisma.

Kara karanta wannan

Mata da miji sunyi karyar yan bindiga sun sace su domin dangi su musu karo-karon naira miliyan 5

A ranar Lahadi ne aka gano sauran sassan jikin mutumin zagaye da kadoji a rafin Olifants da ke Limpopo, a Afrika ta Kudu, MailOnline ta ruwaito.

Kada sunyi kalace da fasto a rafi yayin bikin baftisma.
Kada sunyi kalace da fasto a rafi yayin bikin baftisma. Hoto: Ayzenstayn, FG Trade
Asali: Getty Images

Kada sunyi kalace da fasto a Afrika ta Kudu

Mutumin mai shekaru 48 wanda ya yi ikirarin shi ma'aiki ne ya fito daga yankin Atok, kuma ya nutse a rafin ne yayin da ya ke yin baftisma da wasu mutum biyu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A yayin da suke ibadar, jaridar Vanguard ta ruwaito cewa:

"Wani Fasto daga cikin su ya fara fuskantar matsala a cikin rafin wanda ke tarin kadoji.

Kakakin rundunar 'yan sanda ta yankin, Kanal Malesela Ledwaba, ya sanar da cewa:

"Ana zargin cewa kadojin ne suka farmake shi yayin da ya ke baftisma."

Yan sanda sun ce daya daga cikin malaman addinin da suka je rafin sun yi kokarin nemo dan uwansu da ya nutse amma ba su ganshi ba.

Kara karanta wannan

An gano ramin karkashin kasa inda masu garkuwa suke ajiye wadanda suka sace a Najeriya

An gargadi mutane da shiga rafukan kadoji

Haka zalika, shugabannin 'yan sanda sun nemi mazauna yankin da su guji shiga rafukan da suka san akwai kadoji a ciki.

Ahalin kadar 'Nile' na daga cikin alhalin kadojin da ke a Afrika ta Kudu, kuma suna son yin rayuwa a cikin sabbin rafuka.

Daruruwan mutane ne kadoji ke kashewa a kowacce shekara a fadin Arika, inda da yawan lokuta ake gaza kai rahoton faruwar lamarin

An gabza fada tsakanin mayakan ISWAP da Boko Haram

A wani labarin kuma, an gabza kazamin fada tsakanin kungiyoyin 'yan ta'adda na ISWAP da Boko Haram a tsibirin Tumbun Rago da ke Tafkin Chadi.

An ruwaito cewa mayakan ISWAP ne suka kai farmakin domin rama harin da Boko Haram suka kai masu kwanaki baya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel