Labari mai dadi: Mahaddata Al-Qur'ani mai tsarki na kara yawa a kasashen Turai
Rahotanni sun kawo cewa a shekarar 2010 masallacin Salimiye na Amsterdam babban birnin kasar Holan ta fara gudanar da wani shiri na musamman inda take gudanar da wani shiri na musamman ta fannin rainon yara tare da kokarin ganin sun haddace littafi mai tsarki wato Al-qur’ani.
Ta yi nasara akan wannan kudiri na ta domin zuwa yanzu rahotanni sun nuna cewa sama da yara matasa 20 ne suka khattama haddar su.
Limamin Masallacin na Salimiye Hafiz Ahmad Kaya ya bayyana cewa, nan da wani lokaci za su gudanar da hanyoyin Koyar da Haddar a sauran manyan masallatan kasar ta Holan.
A shekarar bara ne wani yaro mai shekaru 14 Amir Kurban ya kammala haddarsa a Masallacin na Salimiye inda ya bayyana cewa abu ne mai dadi da shauki mutum ya haddace Alkur'ani mai tsarki.
KU KARANTA KUMA: Gwamna Badaru ya yi wa matar da ta haifi yan hudu sha tara ta arziki (hotuna)
Limamin Masallacin Juma'a na Mevlana da ke Amsterdam Hafiz Abdullah Kayın ya ce, suna da burin kafa irin wadannan makarantu na Haddar Al-qur'ani a Kasashen Turai baki daya.
Akwai dalibai 814 da suka hada da mata 560 da suke karatu a cibiyoyin haddar Alkur'ani na kasashen Turai baki daya karkashin kulawar hukumar Diyanet ta Turkiyya da kuma Kungiyar Al'Umar Musulmi ta IGMG.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng