Allahu Akbar: Wata yarinya mai shekaru 6 ta haddace Qur'ani a UAE

Allahu Akbar: Wata yarinya mai shekaru 6 ta haddace Qur'ani a UAE

Maysam Yahya Mohammed yarinya ce mai shekaru 6 a duniya, asalinta ‘yar kasar daular Larabawa ta UAE. Ta kammala haddace al-Qur’ani mai girma tare da Tajweed tana da shekaru 6 a duniya. A halin yanzu, ita ce mutum mafi kankanta da ta haddace Qur’ani a kasar.

Kamar yadda mahaifiyarta tace, “Ta kammala haddace surori 3 na Qur’ani a lokacin da take da shekaru 3 kacal a duniya. Ta fara haddace sauran surorin ne bayan da aka mikata Sharjah Foundation. Ta yi nasarar zama ta 7 a gasar mahaddata da Sheikh Zayad ya shirya a lokacin da take shekaru 3. Kuma ta shiga gasar ne a matsayin mafi kankanta.”

DUBA WANNAN: Kunne ya girmi kaka: Alakar sarautar 'Sarkin Bai' da jihadin Shehu bin Fodio

Dukkan godiya ta tabbata ga Ubangiji, don kuwa ta kammala haddace Qur’ani kafin ta shiga makarantar boko. Babban abinda ya taimaka wajen samun wannan gagarumar nasarar shi ne yadda Maysam ke sauraron karatun Qur’ani kuma tana maimaitashi.

An mikata zuwa masallacin Khorfakkan inda ta koyi dokokin karatun al-Qur’ani kuma ta cigaba da hadda.

Gidan rediyon Qur’ani na masarautar Sharjah ya karramata. Ta samu lambar yabo daga wata tsangayar haddace Qur’ani ta duniya da ke Dubai.

Tsangayar ta kware wajen shirya gasa don karin karfin guiwa ga mahaddatan al-Qur’ani da shirya taro da suka danganta da mahaddata. Sukan hada kan mutane ballantana matasa wajen koya musu Qur’ani.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel