Jerin matan arewa guda 5 da suka yi fice wajen kare hakkin Dan Adam a duniya
- An ware kowacce ranar 10 ga watan Disamba ta shekara don bikin kare hakkin dan Adam
- Fafutukar kare hakkin mata kuwa na daga cikin hakkokin dan Adam
- Akwai mata masu tsananin gwarzanta da suka taka rawar gani wajen kare hakkin mata a arewacin Najeriya
A kowacce ranar 10 ga watan Disamba ne ake bikin kare kare hakkin dan Adam. An amince da ranar ne tun a shekarar 1948. Akwai mata masu yawa da ke fafutukar kare hakkin mata. Ga mata biyar da suka yi fice a wajen kare hakkin dan Adam a arewacin Najeriya.
1. Laila Dogonyaro
Haifaffiyar birnin Kano ce a 1944. An yi mata aure tana da shekaru 13 a duniya. Ta rasu tana da shekaru 66 a shekarar 2011.
Hajiya Laila ta shahara wajen fafutukar kare hakkin mata, musamman ganin an ilimantar da su.
Ta shugabanci kungiyoyin mata daban-daban. Kafin nan kuwa, tana cikin matan da suka kirkiri jam'iyyar matan Arewa da nufin taimaka wa iyalai matalauta a arewacin Najeriya.
2. Hafsat Baba
An haife ta ne a 1957 kuma ta shahara wajen fafutukar kare hakkin mata wadanda suka rasa mazajensu da kananan yara, musamman marayu.
Ta yi kwamishinar kula da ayyukan jin kai da walwalar al'umma a jihar Kaduna. Kafin nan, ta rike mukamin kwamishinar mata.
3. Saudatu Mahadi
Mace ce mai fafutukar kare hakkin mata da kwato 'yancinsu a Najeriya.
Ta taba zama mamba a majalisar gudanarwa ta hukumar kare hakkin dan Adam a Najeriya. Tana daga cikin matan da suka assasa yekuwar Bring Back Our Girls da nufin zaburar da hukumoni don ceto 'yan matan Chibok.
4. Maryam Awaisu
Marubuciya ce kuma mai fafutukar kare hakkin mata. Tana daga cikin matasan mata da suka assasa yekuwar #ArewaMeToo. Kungiyar na karfafa guiwar wadanda aka taba yi wa fyade su fito su fada don a dauki mataki.
5. Hassana Maina
Ta karanci aikin lauya a jami'ar Ahmadu Bello ta Zaria. Matashiyar mai shekaru 21 da haihuwa jigo ce a fafutukar #NorthNormal. Kungiyar na da burin ganin jihohin Najeriya sun haramta cin zarafin jama'a a cikin kundin dokokinsu.
A yanzu haka, tana jagorantar wani shiri na wayar da kan yara 'yan makaranta game da cin zarafi ta hanyar lalata.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng