An Kashe Rayuka Sama da 30 Yayin da Mahara Suka Ci Gaba da Halaka Bayin Allah a Jihar Arewa

An Kashe Rayuka Sama da 30 Yayin da Mahara Suka Ci Gaba da Halaka Bayin Allah a Jihar Arewa

  • Ƴan ta'adda sun ci gaba da kashe bayin Allah a karamar hukumar Mangu ta jihar Filato duk da sanya dokar hana fita ta sa'o'i 24
  • Rahoto ya nuna cewa mutanen da ba su gaza 30 ba sun rasa rayuwarsu yayin da ƴan bindiga suka shiga wani kauye da safiyar Laraba
  • Gwamna Celeb Mutfwanga ya sanar da sa dokar zaman gida a faɗin yankin Mangu ranar Talata amma kashe-kashen bai lafa ba

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Plateau - Rahotanni sun nuna cewa an ci gaba da kashe bayin Allah da ƙona gidaje a ƙaramar hukumar Mangu da ke jihar Filato duk da dokar hana fita da gwamnati ta sanya.

Kara karanta wannan

Ana fargabar rayukan mutane da dama sun salwanta a wani sabon rikici a jihar Arewa

Gwamna Celeb Mutfwang ya ƙaƙaba dokar zaman gida ta tsawon awanni 24 a sassan ƙaramar hukumar bayan kashe-kashen da ya afku jiya Talata, Daily Trust ta ruwaito.

Gwamna Celeb Mutfwang na jihar Plateau.
Sama da mutum 30 sun mutu yayin da ake ci gaba da kashe bayin Allah a jihar Plateau Hoto: Celeb Mutfwang
Asali: Facebook

Duk da haka tashin hankalin bai lafa ba yayin da mazauna garin Mangu suka tabbatar da cewa ‘yan bindiga sun afkawa kauyuka, inda suka buɗe wuta kan mai uwa da wabi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jaridar Punch ta tattaro cewa aƙalla mutane 30 aka kashe yayin da ƴan bindigan suka shiga kauyen Kwahaslalek da ke ƙaramar hukumar Mangu da safiyar yau Laraba.

Suleiman Muhammad, mazaunin Mangu ya ce:

"Da misalin karfe 9:30 na safiyar yau ne wasu ‘yan bindiga dauke da manyan makamai suka zo suka buɗe wuta, sun kona gidaje da yawa ciki har da Islamiyya. Sannan sun kashe mutane.
"Sun ci ƙarfin jami'an tsaro da ke Mangu, yanzu haka zagaye muke da ƴan bindiga."

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun sace mata da miji da yaransu a Kaduna

An kashe mutum 10 a wani ƙauye

The Nation ta tattaro cewa ƴan bindiga sun kashe mutane akalla 30 a kauyen Kwahaslalek da ke karkashin Mangu, in ji wani shugaban al'umma.

Mutumin mai suna, Mark Haruna ya ce:

"Abin da ya faru a Sabon Gari da Garin Mangu a jiya da rana (Talata) an yi ne domin ɗauke hankalin jama’a daga kauyuka. Jiya da tsakar dare aka kai hari kauyen mu Kwahaslalek."
"Ƴan bindigan sun shiga kauyen da ƙarfe 12:30 na wayewar garin Laraba inda suka halaka mutane sama da 25, mafi yawa mata da ƙananan yara."

Gwamnoni sun ɗauki zafi kan satar mutane

A wani rahoton kuma wasu gwamnonin Arewa da takwarorinsu na kudu sun shirya zartar da hukuncin kisa kan duk wanda aka kama da laifin garkuwa da mutane.

Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf na ɗaya daga cikin waɗannan gwamnoni guda 9 kuma Legit Hausa ta tattaro muku su gaba ɗaya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel