Wadanda Su Ka Ci Bashin Korona Sun Koka Kan Shirin Kwato Kudaden Da CBN Ke Yi

Wadanda Su Ka Ci Bashin Korona Sun Koka Kan Shirin Kwato Kudaden Da CBN Ke Yi

  • Shugaban kasa, Bola Tinubu ya umarci bankin CBN da DSS su kwato kudaden lamunin da aka bai wa 'yan Najeriya a 2020
  • Bankin ya fara zaftare kudade a asusun bankunan wadanda su ka ci wannan gajiya a 2020 a kokarin kwato kudaden daga hannun jama'a
  • Mutane da dama daga cikin wadanda su ka ci gajiyar shirin sun koka kan yadda ake cire musu kudade a asusun bankunan su

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT, Abuja - Babban Bankin Najeriya, CBN ya shirya kwato kudaden da ya bai wa 'yan Najeriya bashi don rage talauci.

Bankin ya ba da lamunin ne don rage radadin da jama'a su ka shiga saboda annobar 'Corona' a 2020, Daily Nigerian ta tattaro.

CBN ya shirya kwato kudaden lamunin 'Covid-19'
Bankin CBN ya fara kwashe kudade a asusun bankuna. Hoto: Central Bank of Nigeria.

Meye wadanda su ka ci gajiyar ke cewa kan CBN?

Kara karanta wannan

Ana Rade-radin Bankin CBN Zai Maida $1 Ta Zama N1.25, Dala Ta Koma N930

Mafi yawan wadanda su ka ci gajiyar kudaden na korafin yadda ake kokarin kwato kudaden daga gare su.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wata daga cikin wadanda su ka ci gajiyar, Fatima Alli ta ce yadda babu shiri ake kokarin karbar Naira dubu 500 daga gareta ya kara jefa ta cikin matsalar kudi.

Ta ce:

"Na samu lamunin Korona a 2020 wanda a lokacin aka ce ba za mu biya ba.
"Amma a yanzu duk kudin da ke asusun banki na an kwashe saboda biyan wadannan kudaden."

Wane martani mutane ke yi kan CBN?

Wani mai suna Abbas Sule ya koka da cewa duk kudaden asusun bankinsa an kwashe, cewar Tribune.

Ya ce:

"Lokacin da aka ba ni bashin Naira dubu 500, bankin ya cire Naira dubu 50 wanda hakan ya saka aka ba ni Naira dubu 450.

Kara karanta wannan

Tiriliyan 87 Na Bashin Najeriya, Tinubu Ya Gaza Tabuka Komai, An Bayyana Wadanda Ke Bin Kasar Bashi

"Kuma a yanzu su na so na biya Naira dubu 500, wannan ba adalci ba ne."

'Ba manoma ba ne su ka ci kudin lamuni', AFAN ga CBN

A wani labarin, Kungiyar Manoma a Najeriya, AFAN ta bayyana cewa mafi yawan wadanda su ka ci gajiyar kudaden noma ba manoman asali ba ne.

Kungiyar ta ce kwato wadannan kudade a hannun jama'a zai yi matukar wahala ganin yadda aka yi abin ba tsari.

Wannan na zuwa ne bayan Shugaba Tinubu ya umarci CBN da DSS su kwato kudaden lamuni da aka bai wa 'yan Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.

Online view pixel