EFCC: Yadda Shugabar Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya Tayi Gaba da Kudi Tana Ofis
- Winifred Oyo-Ita tana shari’a da hukumar EFCC bisa zargin cin wasu kudi ta hanyar da ta saba doka
- Wani da ya bada shaida ya zargi jami’ar da samun kwangila a kamfaninta yayin da take kan mukami
- Daga baya Oyo-Ita ta zama shugabar ma’aikatan gwamnatin tarayya a mulkin Muhammadu Buhari
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.
Abuja - Wani mai bada shaida da hukumar EFCC ta gayyato, ya bayyana a gaban kotu a shari’ar gwamnati da Misis Winifred Oyo-Ita.
The Nation ta ce Hamma-Adama Bello ya shaidawa kotun tarayya da ke Abuja yadda Winifred Oyo-Ita ta wawuri dukiyar gwamnati.
Winifred Oyo-Ita v EFCC
Hamma-Adama Bello ya yi bayanin yadda tsohuwar shugaban ma’aikatan gwamnatin tarayya ta ci kudi ta hanyar kamfanoni.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mai bada shaidan wanda babban jami’in EFCC ne kuma shugaban sashen bincike na SIT ya yi bayani a gaban Alkali James Omotosho.
EFCC ta kawo shaidu a kan Oyo-Ita
Ma’aikacin na EFCC shi ne shaida na takwas da hukumar ta kawowa kotun da ke Abuja.
Lauyan hukumar EFCC mai yaki da rashin gaskiya, Farouk Abdullah ya jagoranci Hamma-Adama Bello wajen yin shaidar abin da ya sani.
Wata rana yana ofis a 2019, Hamma Bello yace ya samu rahoton wasu abubuwa da Oyo-Ita suke yi a lokacin ita tana babbar sakatariya.
Wanda ake tuhuma ta rike wannan mukami a ma’aikatar harkoki na musamman da sha’anin gwamnati a mulkin Muhammadu Buhari.
EFCC ta binciki kamfanonin Oyo-Ita
Mai bada shaidar yace sun gano Oyo Ita da wani hadiminta, Ubong Effiok, sun hada-kai domin neman kwangila a wasu kamfanoni biyu.
Daily Nigerian tace wadanda ake zargi suna da alaka da kamfanonin da aka ba kwangilolin, wanda hakan ya sabawa ka'idojin aiki.
An bada sunayen wadannan kamfanoni biyu da ake bincike da Frontline Ace Global Services Limited da kuma Asanaya Projects Limited.
Shaidan da EFCC ta kawo ya fadawa kotu cewa Oyo-Ita tana da asusu a wani babban banki dauke da kudin Frontline Ace Global Services.
Binciken EFCC ya gano N124m sun shiga asusun sa’ilin tana mataimakiyar darekta a 2020. James Omotosho ya daga shari’ar zuwa Juma’a.
Bola Tinubu yace a kara hakuri
Ana da labari shugaban kasa Bola Tinubu yayi wa ‘yan Najeriya tanadi, yace saura kiris a ci moriyar tsare-tsaren da ya kawo a mulki.
Mai girma Tinubu yace dole ta sa ya dauki tsauraran matakai amma a cewarsa za a ga amfanin hakan nan gaba kadan a gwamnatinsa.
Asali: Legit.ng