Yanzu-yanzu: Buhari ya yi wa Oyo Ita murabus, ya tabbatar da Yemi-Esan a matsayin sabuwar shugaban ma'aikatan tarayya

Yanzu-yanzu: Buhari ya yi wa Oyo Ita murabus, ya tabbatar da Yemi-Esan a matsayin sabuwar shugaban ma'aikatan tarayya

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a daren Juma'a ya amince da murabus din Misis Winifred Ekanem Oyo-Ita a matsayin shugaban ma'aikatan gwamnatin tarayya daga ranar Alhamis 27 ga watan Fabrairun 2020.

Bayan haka, shugaban kasar ya kuma tabbatar da nadin Dakta Folashade Yemi-Esan wacce ta kasance shugaban ma'aikatan tarayyar na wucin gadi a matsayin tabbataciyar shugaban ma'aikatan gwamnatin tarayya (HoCSF).

Sakataren gwamnatin tarayya, Mista Boss Mustapha ne ya sanar da hakan a madadin sakataren dindin na na ofishin GSO, na ofishin sakataren gwamnatin tarayya, Mista Olusegun Adekunle kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Yanzu-yanzu: Buhari ya yi wa Oyo Ita murabus, ya tabbatar da Yemi-Esan a matsayin sabuwar shugaban ma'aikatan tarayya
Yanzu-yanzu: Buhari ya yi wa Oyo Ita murabus, ya tabbatar da Yemi-Esan a matsayin sabuwar shugaban ma'aikatan tarayya
Asali: Facebook

DUBA WANNAN: Sojoji sun kama 'yar bindiga 'na rawa da AK-47 rataye a wuyar ta' a Kaduna

Hakan na zuwa ne watanni biyar bayan an dakatar da Oyo-Ita daga kujerarta a kan zargin aikata rashawa.

An dakatar da Oyo-Ita daga kujerar ta ne a ranar 18 ga watan Satumban 2019 bayan da aka mika wani rahoton zargin ta da hannu cikin bayar da wasu kwangila daga ofishinta ba bisa ka'ida ba.

A cewar sanarwa na amincewa da murabus din nata, Shugaba Buhari ya ce za a cigaba da binciken zargin da ake mata na hannu cikin aikata rashawar.

Shugaban kasar ya yi mata godiya bisa aikin da ta yi wa kasar ta kuma ya yi mata fatan alheri a ayyukan da za ta yi a gaba.

Shugaban kasar ya yi amfani da ikon da doka ta bashi wurin nada Dakta Misis Folashade O. Yemi-Esan a matsayin sabuwar shugaban ma'aikatan na tarayya.

Yemi Esan ta yi aiki a ma'aikatu da damu da suka hada da ma'aikatan sadarwa, ma'aikatan ilimi, ma'aikatan man fetur da kuma ofishin shugaban ma'aikatan na tarayya.

Shugaban kasar ya bukaci sabuwar shugaban ma'aikatan ta yi amfani da kwarewar ta wurin kawo cigaba da na bayan ta suka fara.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel