Labari cikin hotuna: Shugaba Buhari ya gana da mukaddashin shugabar ma’aikatan tarayya
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gana da mukaddashin shugabar ma’akatan tarayya, Misis Folashade Yemi Esan a fadar Shugaban kasa, Abuja.
A cikin ganawar wanda ya gudana a yau Juma’a, 20 ga watan Satumba harda babban sakataren tarayya, Boss Mustapha.
Ga hotunan haduwar nasu a kasa:
Idan da za ku tuna a ranar Laraba, 18 ga watan Satumba ne shugaban Buhari, ya amince da nada Folashade a matsayin mukaddashin shugabar hukumar kula da ma'aikatan gwamnatin tarayya.
KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Atiku ya rubuta budaddiyar wasika zuwa ga yan Najeriya, ya sha alwashin samun nasara a kotun koli
Dakta Folashade, wacce babbar sakatariya ce a ma'aikatar albarkatun man fetur, ta maye gurbin Winifred Oyo-ita, wacce aka umarta da tafiya hutun dole maras iyaka domin bawa hukumar yaki da cin hanci da karya tattalin arziki (EFCC) kammala binciken da ta fara a kanta.
A halin da ake ciki Legit.ng ta rahoto a baya cewa a ranar Alhamis, jami'an tsaro suka zagaye ofishin shugaban ma'aikatan tarayya. Kasa da sa'o'i 12 bayan da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya umarci tsohuwar shugabar ma'aikatar, Winifred Oyo-Ita da ta bar aiki.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng