NSCIA ta nada sabon mataimakin shugaba

NSCIA ta nada sabon mataimakin shugaba

- Kungiyar ci gaban harkokin addinin musulunci ta sanar nada Alhaji Rasaki Oladejo a matsayin sabon mataimakin shugaba

- Oladejo wanda kwarrarre ne a fannoni da dama ya maye gurbin marigayi Alhaji S. O. Babalola wanda ya rike mukamin har zuwa 2 ga Oktoba 2019 lokacin rasuwar sa

- Oladejo ya rike mukamai da dama daga ciki akwai shugabancin Nawair-Ud-Deen daga 2013 zuwa 2019

Majalisar Kolin harkokin addinin musulunci (NSCIA) karkashin jagorancin shugaban ta sarkin musulmi, Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar III, ta nada Alhaji Rasaki Oldejo, a matsayin mataimakin shugaba (daga yankin kudu) na kungiyar.

Mataimakin sakatare, NSCIA, Prof. Salisu Shehu ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar a shafin Facebook na Majalisar a ranar Alhamis 24 ga watan Disambar 2020.

NSCIA ta nada sabon mataimakin shugaba
NSCIA ta nada sabon mataimakin shugaba. Hoto: @daily_trust
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Masu garkuwa sun kai hari Kano, sace dan kasuwa sun kuma kone motar 'yan sanda

Ya ce Alhaji Oladejo ya maye gurbin marigayi Alhaji S. O. Babalola, wanda shi ne a mukamin kafin rasuwar a ranar 2 ga Oktoba, 2019.

A cewar sa, Oladejo, wanda ba'a dade da nada shi matsayin shugaban al'ummar musulmin Najeriya yankin kudu maso yamma (MUSWEN), babban jagoran addini ne, masanin tattalin arziki, malamin addinin musulunci, kuma mamba ne a kwarrarrun makarantu.

"Shi ne shugaban kwamitin tattalin arziki, kudade da tsare tsaren ci gaba daga watan Mayu 2013 zuwa Nuwamba 2014.

KU KARANTA: Sirrin cin galaba kan 'yan bindiga a Arewa yana Zamfara, in ji Matawalle

Kuma shine shugaban kungiyar Nawair-Ud-Deen na kasa (wata kungiyar addinin musulunci da aka kafa a 1939) daga 2013 zuwa 2019.

Shine shugaban, Mountain Investment and securities Limited, mamba daga hukumar chanjin kudade," a cewar Shehu.

A baya, kun ji cewa gwamnatin jihar Zamfara ta ware naira biliyan 1 a kasafin 2021 don ginawa da gyara masallatan juma'a, makarantun islamiyya, makabartu, wuraren wa'azi da sauran harkokin addini.

Kwamishinan harkokin addinan jihar, Sheik Tukur-Jangebe ne ya bayyana haka, lokacin da ya ke zantawa da manema labarai ranar Juma'a bayan gabatar da kasafin ma'aikatar na 2021 ga majalisar dokokin jihar Zamfara.

Jangebe ya shaida cewa gwamnatin Zamfara ta tsara ayyukan ci gaba a karkashin ma'aikatar addinin musulunci a 2021.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Online view pixel