Tsadar Rayuwa: Jihohi 10 Da ’Yan Najeriya Ke Shan Tsada Wajen Siyar Gas Din Girki

Tsadar Rayuwa: Jihohi 10 Da ’Yan Najeriya Ke Shan Tsada Wajen Siyar Gas Din Girki

  • ‘Yan Najeriya sun sake gamuwa da karin farashin gas din girki yayin da farashinsa ya tashi sama da yadda aka saba siya a kasuwa
  • Wasu sabbin bayanai daga hukumar NBS sun bayyana cewa, an samu karin 8.70% a gas mai nauyin 12.5k sai kuma Karin 12.31% a mai nauyin 5kg
  • Bincike ya nuna yankunan Arewa maso Gabas ne suka fi fuskantar tsadar gas din girki a yayin da farashin kayayyaki ke kara hawa

Salisu Ibrahim kwararren editan fasaha, kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas.

Hukumar kididdiga ta Najeriya (NBS) ta bayyana sabon farashin iskar gas din girki da ‘yan Najeriya ke siya a kasuwa.

A cewar rahoton, ‘yan kasar sun ga Karin farashi sabanin yadda suka saba siya a kasuwanni a lokutan bayan kadan da suka gabata.

Kara karanta wannan

Bincike ya gano jihohin Najeriya 10 da aka fi samun man fetur da araha

Yadda farashin iskar gas din girki yake a wasu jihohi
Yadda gas din girki yake a wasu jihohin Najeriya | Hoto: Nurphoto
Asali: UGC

Yadda kididdigar take

Legit ta naqalto daga NBS cewa, 5kg na gas din girki ya samu Karin akalla 2.79% a matakin wata-wata daga N4,828.18 a watan Nuwamban 2023 zuwa N4,962.87 a watan Disamban 2023.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A matakin shekara-shekara, 5kg na gas ya karu da 8.70% daga N4,565.56 a watan Disamban 2022.

Rahoton ya bayyana cewa, gas mai nauyin 12.5kg ya samu karin 3.18% a matakin wata-wata, daga N11,155.15 na watan Nuwamban 2023 zuwa N11,510.16 a watan Disamban 2023.

A matakin shekara-shekara, gas mai nauyin 12.5kg ya karu da 12.31% daga N10,248.97 a watan Disamban 2022.

Jihohin da aka fi tsadar da arahar gas

A cewar NBS, jihar Adamawa ce ta fi kowacce jiha tsadar iskar gas, inda ake siyar da 5kg a farashin N5,725.33 sai kuma Jigawa da ake siyar da gas din N5,686.88 da kuma Legas mai N5,671.05.

Kara karanta wannan

Wata mata ta sheke abokin 'sharholiyarta' bayan da ya nemi karin lalata da ita

A gefe guda, jihohin da aka fi arahar gas sun hada da Ebonyi da ake samun 5kg a N4,071.43 sai kuma Imo da Abia N4,088.24 and N4,155.88 bi da bi.

Jihohi 10 da aka fi tsadar gas

  1. Cross River - N13,572
  2. Edo - N13,265
  3. Delta - N13,041
  4. Jigawa - N12,909
  5. Benue - N12,720
  6. Kogi - N12,700
  7. Nasarawa - N12,445
  8. Ekiti - N12,556
  9. Yobe - N12,000
  10. Kwara - N11,992

Jihohin da suka fi arahar man fetur

A wani labarin, kididdigar hukumar NBS ta bayyana alkaluman farashin man fetur a Najeriya da yadda aka siyar dashi zuwa karshen watan Disamban bara; 2023.

A cewar kididdigar, an siyar da man fetur a kan farashin N671.86 a watan Disamban shekarar da ta gabata ta 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel