Dukiyar Aliko Dangote Ta Karu da Sama da Naira Biliyan 510 a Rana Daya, an Gano Dalili

Dukiyar Aliko Dangote Ta Karu da Sama da Naira Biliyan 510 a Rana Daya, an Gano Dalili

  • Daga sanar da cewa matatar man Dangote ta fara aiki, har an samu tururuwar masu saka hannun jari a rukunin kamfanonin sa
  • A makon da ya gabata ne Aliko Dangote ya sanar da cewa matatar mansa ta fara aiki kuma za ta rinka tace ganga 650,000 a kowacce rana
  • Bayan sanarwar, an ga yadda wasu sassa uku na rukunin kamfanonin ya samu karuwar daraja ta naira biliyan 513.69 a ranar Litinin

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Bayan sanar da cewa matatar man Dangote ta fara aiki, masu saka hannun jari sun garzaya zuwa kasuwar canji ta Najeriya don siyan hannayen jari na rukunin Dangote.

Bayan haka, darajar wasu rassa uku na rukunin Dangote da aka saka a kan kasuwar hada-hadar kudi ta Najeriya (NGX) ta karu da naira biliyan 513.69 a ranar Litinin.

Kara karanta wannan

FG ta saki sunayen kamfanonin Najeriya da suka cancanta su nemi kwangilar gwamnati a 2024

Dangote ya samu ribar N514bn a rana daya
Bayan fara tace man fetur, Dangote ya samu ribar naira biliyan 514 a rana daya. Hoto: Bloomberg, @DangoteGroup
Asali: UGC

Batu kan saka hannun jarin 'yan kasuwan da kuma karuwar darajar rassan guda uku ya biyo bayan sanar da fara tace danyen mai a matatar man Dangote, Daily Trust ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Zuwa karshen watan Janairu man matatar Dangote zai shiga kasuwa

Idan ba a manta ba, a ranar Juma’ar da ta gabata ne wani faifan bidiyo ya nuna matatar man da za ta rinka tace ganga 650,000 a kowace rana ta fara aikin tatar man gadan-gadan.

Da yake magana game da ci gaban, Aliko Dangote, shugaban rukunin Dangote, ya bayyana matatar a matsayin babbar nasara ga kasa Najeriya.

Dangane da lokacin da man matatar zai shiga kasuwa, Vanguard ta ruwaito Dangote ya ce zai shiga kasuwa kafin karshen watan Janairu da zarar ya samu amincewar doka.

Kara karanta wannan

Jerin manyan kamfanoni 7 da suka amince za su yi dillancin mai a matatar Dangote

Matatar man Dangote ta cika dukkan ka'idoji na fasahar duniya

Rahotanni sun ce ya zuwa yanzu matatar ta samu ganga miliyan shida na danyen mai a rumbun ajiya guda biyu da ke da nisan kilomita 25 daga gabar teku.

An fara sauke danyen mai na farko ne a ranar 12 ga Disamba, 2023, kuma an sauke jirgi na shida a ranar 8 ga Janairu, 2024, in ji Dangote.

Tsarin matatar ya dace da ka'idojin Bankin Duniya, US EPA, ka'idojin fitar da hayaki na turai, da ka'idojin fitar da mai na kasar, ta hanyar yin amfani da fasahar zamani.

Manyan kamfanoni 7 za su fara dillancin man Dangote

A wani labarin kuma, manyan kamfanonin Najeriya 7 sun yi rijista don fara kasuwancin man matatar Dangote.

Haka zalika, kungiyar dillalan man fetur ta kasa su ma sun ce sun kammala shiri na tattaunawa da matatar man Dangote don fara dillancin man.

Asali: Legit.ng

Online view pixel