Daga Karshe An Bayyana Dalilin da Ya Sanya Ake Kashe-Kashe a Plateau

Daga Karshe An Bayyana Dalilin da Ya Sanya Ake Kashe-Kashe a Plateau

  • Wani tsohon ɗan majalisa, Dachung Musa Bagos, ya ce kisan da ake yi a jihar Playeau tsantsar kisan ƙare dangi ne da kuma ƙwacen ƙasa
  • Bagos ya ce ɓarayin filaye na amfani da waɗannan ƙauyuka wajen haƙo ma’adinai da noma ba bisa ƙa’ida ba
  • Ya ce kashe-kashen da rashin tsaro ba su da alaƙa da rikicin labilanci, addini, ko rikicin manoma da makiyaya a jihar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jos, jihar Plateau - Tsohon ɗan majalisar wakilai mai wakiltar Jos ta Kudu/Jos ta Gabas, Dachung Musa Bagos, ya yi magana game da kashe-kashen da ake yi a jihar Plateau.

Bagos ya ce, kashe-kashen da rashin tsaro na faruwa ne sakamakon ɓarayin filaye da ke amfani da waɗannan ƙauyuka wajen haƙo ma’adinai da noma ba bisa ƙa’ida ba.

Kara karanta wannan

Ana cikin jimamin hare-haren Plateau, yan bindiga sun kai sabon hari a jihar Arewa

Dachung ya yi magana kan kashe-kashen Plateau
Dachung ya ce masu kwace filaye ne ke kashe-kashe a Plateau Hoto: Dachung Musa Bagos
Asali: Facebook

Ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da gidan talabijin na Arise tv a ranar Juma’a, 26 ga watan Janairu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Meyasa ake kashe-kashe a Plateau?

Tsohon ɗan majalisar ya bayyana cewa babu batun rikicin ƙabilanci, addini, ko rikicin manoma da makiyaya a jihar.

A kalamansa:

"Abin da ke faruwa shine tsantsar kisan ƙare dangi da ƙwacen ƙasa. Mutane suna shiga cikin ƙauyuka, suna kashewa, suna korar mutanen kuma suna mamaye filayensu. Kuma ba magana ce kawai ba, hujjoji suna nan."
"Babban manufar da muka gano, kuma idan aka yi la’akari da tarihin duk ƙauyukan da aka lalata a Plateau, kowane ɗaya daga cikinsu yana da ƙarfin tattalin arziki ɗaya ko biyu a Plateau.

Ya ƙara da cewa:

"Jeka wasu daga cikin waɗannan ƙauyukan, za ka ga cewa suna da ciyayi sosai da za ka iya noma a can, kana iya kiwon shanu a can, suna da koguna. Don haka, duk waɗannan ƙauyukan ana yi musu hakan ne don wata manufa."

Kara karanta wannan

Ana fargabar rayukan mutane da dama sun salwanta a wani sabon rikici a jihar Arewa

An Sassauta Dokar Hana Fita a Plateau

A wani labarin kuma, kun ji cewa Gwamna jihar Plateau, Caleb Mutfwang, ya sassauta dokar hana fita da ya sanya a ƙaramar hukumar Mangu ta jihar.

Gwamnan ya ɗauki matakin sassauta dokar hana fitan ne biyo bayan yadda lamuran tsaro suka inganta a ƙaramar hukumar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel