Jerin jihohi 10 da suka fi yawan marasa aikin yi a Najeriya
- Kamfanin BudgIT ya fitar da rahoton State of States na 2021 na jihohin da suka fi yawan marasa aikin yi a Najeriya
- A bisa ga rahoton, bakwai daga cikin jihohin sun kasance daga yankin arewa yayin da sauran ukun suka kasance a yankin kudu
- Jihar Imo ita ce ta farko a wannan rukunin inda take da kaso 82.54 cikin 100 na marasa aiki
Rahoton State of States na 2021 da kamfanin BudgIT ya wallafa ya nuna rabe-raben matakin aikin yi a jihohin Najeriya.
Har ila yau, rahoton wanda aka wallafa kwanan nan ya ambaci Ofishin Kididdiga na Kasa (NBS) a matsayin tushensa.

Source: Facebook
Legit.ng ta lissafa manyan jihohi 10 da suka fi yawan marasa aikin yi a bisa rahoton.
1. Jihar Imo - 82.54%

Kara karanta wannan
Katsina: ‘Yan sanda sun kama tsohuwar ma’aikaciyar hukumar NIS bisa damfara ta N47m
2. Jihar Jigawa - 79.98%
3. Jihar Adamawa - 79.56%
4. Jihar Yobe - 74.12%
5. Jihar Cross River - 71.46%
6. Jihar Kogi - 67.78%
7. Jihar Taraba - 67.72%
8. Jihar Akwa Ibom - 67.69%
9. Jihar Borno - 67.10%
10. Jihar Kaduna - 67.00%

Source: UGC
Bakwai daga cikin jihohin da ke cikin jerin sun fito ne daga yankin arewa yayin da sauran ukun suka fito daga kudu.
Rashin Aikin Yi: Kana cikin waɗan da suka jawo Najeriya ta zama haka, Adesina ya maida ma Atiku Martani
A wani labarin, Mista Femi Adesina, mai baiwa shugaban ƙasa shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai, ya ce tsohon shugaban ƙasa Atiku Abubakar na cikin waɗan da suka ɓata Najeriya.
A martani da ya maida masa kan magan-ganun da ya yi kwanan nan, Adesina ya ce "Atiku ba zai iya tsame hannunsa daga yadda Najeria ta zama ba."

Kara karanta wannan
Zangon karatu na 2021/2022: Jerin jami'o'in da suka sanar da ranakun zana jarabawar Post UTME
Atiku, wanda shine ɗan takarar shugaban kasa ƙarkashin jam'iyyar PDP a zaɓen 2019, ya ce a ƙarƙashin mulkin Buhari Najeriya ta kama hanyar lalacewa.
Asali: Legit.ng