Jerin Jihohi 10 Da Suka Fi Tsadar Rayuwa a Najeriya

Jerin Jihohi 10 Da Suka Fi Tsadar Rayuwa a Najeriya

  • Kimanin jihohi 10 a Najeriya ne suka zama jihohin da suka fi ko ina tsadar rayuwa kamar yadda alƙaluman hauhawar farashin kayayyaki suka nuna
  • Hakan na zuwa ne a sakamakon sabbin alƙaluman hauhawar farashin kayayyaki da hukumar ƙididdiga ta kasa ta fitar
  • Rahoton ya nuna cewa jihohin Kogi, Legas da Rivers ne aka fi samun hauhawar farashin abinci a Najeriya

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Sabuwar ƙididdigar farashin kayayyakin masarufi da hukumar ƙididdiga ta ƙasa (NBS) ta fitar, ya nuna cewa jihohin Kogi, Legas, da Rivers na daga cikin jihohin da suka fi tsadar rayuwa, bisa alƙaluman hauhawar farashin kayayyaki na watan Agustan 2023.

A duk shekara, jihar Kogi ce ke kan gaba wajen samun hauhawar farashin kayayyaki da kaso 31.50%, sai Legas da kaso 29.17% sai Rivers da kaso 29.06.

Jihohin da suka fi tsadar rayuwa a Najeriya
Kogi, Legas da Ribas sun fi ko ina tsadar rayuwa a Najeriya Hoto: Bloomberg / Contributor
Asali: Getty Images

Babu tsadar rayuwa sosai a jihohin Sokoto, Borno, da sauran su

Sai dai, Sokoto ta samu kusan kaso 20.91%, Borno ta samu kaso 21.77%, sai kuma Nasarawa mai kaso 22.25%, wanda hakan ya nuna samun raguwar hauhawar farashin kayayyaki a shekara.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A wata, jihohin Kwara, Osun, da Kogi sun samu hauhawar farashin kayayyaki a watan Agusta, yayin da jihohin Sokoto, Borno, da Ogun suka samu raguwar hauhawar farashin kayayyaki.

Hauhawar farashin kayan abinci a watan Agustan 2023 ya nuna irin wannan yanayin, inda Kogi ke kan gaba da hauhawar farashin kayan abinci a kowace shekara da kaso 38.84%, Legas ta zo na biyu da kaso 36.04%, sai Kwara mai kaso 35.33%.

Sokoto ta samu hauhawar farashin kayan abinci da kaso 20.09%, Nasarawa da kaso 24.35%, sai Jigawa da kaso 24.53% duk shekara.

Jaridar Punch ta rahoto cewa duk wata jihohin Rivers, Kwara, da Kogi suna samun hauhawar farashin kayan abinci, yayin da jihohin Sokoto, Abuja da Neja ke samun raguwar hauhawar farashin kayan abinci.

Rahoton jaridar Punch ya ce rahoton na NBS ya nuna cewa hauhawar farashin kayan abinci ya samo asali ne sakamakon tsadar kayan masarufi da suka haɗa da mai, burodi, hatsi, kifi, ƴaƴan itace, nama, kayan lambu da dankali.

Magidanta Sun Fara Satar Amfanin Gona

A wani labarin kuma, tsadar rayuwa ta sanya wasu magidanta koma wa satar kayan amfanin gona domin ciyar da iyalansu a jihar Taraba.

Daga cikin kayayyakin da ake yawan sata a gona akwai rogo da masara da doya wanda hakan bai rasa nasaba da irin halin kunci da ake ciki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel