Babbar Kotu Ta Yanke Wa Wasu Hatsabiban Yan Bindiga 3 Hukunci Mai Tsauri, Ta Jero Abu 4

Babbar Kotu Ta Yanke Wa Wasu Hatsabiban Yan Bindiga 3 Hukunci Mai Tsauri, Ta Jero Abu 4

  • Babbar kotun jihar Ribas mai zama a Fatakwal ta yanke wa wasu ƴan bindiga masu garkuwa da mutane hukunci yau Alhamis
  • Rahoto ya nuna mutum huɗu ne aka gurfanar gaban kotu bisa tuhume-tuhume huɗu da suka shafi satar mutane da kisa
  • Waɗanda ake zargin sun sace marigayi Cif Abbit Ogbobula a watan Yuni, 2017 kuma suka haɗa baki suka kashe shi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Ribers - Wata babbar kotu da ke zamanta a garin Fatakwal, babban birnin jihar Ribas ta kama wasu mutane 3 da aikata laifin yin garkuwa da mutane.

Ko da yake mutane hudu ne aka gurfanar a gaban kotu bisa laifin yin garkuwa da marigayi Cif Abbot Ogbobula a watan Yunin 2017, kamar yadda Channels tv ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Kano: Kotu ta yanke wa wani hukuncin daurin gidan yari kan satar babur

Kotu ta yanke wa masu garkuwa hukuncin kisa.
Kotu Ya Yanke Wa Rikakkun Ƴan Bindiga Hukuncin Kisa a Jihar Ribas Hoto: Court
Asali: Twitter

Amma mutum uku daga ciki ne babbar kotun ta gamsu sun aikata laifin kuma ta yanke masu hukunci, yayin da ragowar ɗayan kuma kotun ta wanke shi daga zargi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mutum ukun aka faɗi sunayensu da Boma Thompson, Emelike Mathias, da Daniel Thanksgod, an same su ne da laifuka hudu.

Laifukan da aka kama su da aikatawa sun hada da hada baki, garkuwa da mutane, hada baki wajen aikata kisa, da kuma kisan marigayi Cif Abbot Ogbobula.

Mai shari’a Monina Danagogo ce ta jagoranci shari’ar wadda aka gudanar a ranar Alhamis, 18 ga watan Janairu, 2024.

Hukuncin da kotu ta yanke wa masu garkuwa 3

Dangane da tuhumar farko (satar mutane), an yanke wa wadanda ake tuhuma na 1, 2 da 4 hukuncin daurin shekaru bakwai a gidan yari ba tare da zabin tara ba.

Kara karanta wannan

Babbar magana: Ƴan bindigan da suka sace shugaban ƙaramar hukuma sun turo saƙo mai ɗaga hankali

Dangane da tuhuma ta biyu (sace marigayi Cif Abbot Ogbobula), an yanke wa wadanda ake kara na 1 da na 2 da na 4 hukuncin kisa ta hanyar rataya.

A tuhuma ta uku (haɗa kai wajen kashe Marigayi Cif Abbot Ogbobula) kotu ta yanke musu hukuncin ɗaurin shekaru 14 a gidan yari ba tare da wani zaɓi na tara ba.

A tuhuma ta ƙarshe kuma (kisan Cif Abbot Ogbobula), an yanke wa wadanda ake tuhuma na 1,2 da na 4 hukuncin kisa ta hanyar rataya ko kuma ta hanyar allura mai kisa.

An gano gawar mutum 5 a Ibadan

A wani rahoton kuma Gwamnatin Oyo karkashin Gwamna Makinde ta yi ƙarin haske kan yawan mutanen da suka mutu a fashewar da ta afku a Ibadan.

Mai ba gwamna shawara na musamman kan tsaro, Fatai Owoseni, ya ce adadin mamatan ya ƙaru zuwa 5 a yau Alhamis da safe.

Asali: Legit.ng

Online view pixel