Ana Rade-Radin Mayar da Shi Kujerar Sarkin Kano, Sanusi II Ya Samu Babban Mukami a Abia

Ana Rade-Radin Mayar da Shi Kujerar Sarkin Kano, Sanusi II Ya Samu Babban Mukami a Abia

  • Gwamnan jihar Abia, Dr Alex Otti ya nada mai girma Muhammadu Sanusi II da wasu mutane 18 matsayin mambobin cibiyar AGEAC a jihar
  • Gwamna Otti ya ce ya kafa cibiyar AGEAC ne don farfadowa tare da bunkasa kasuwanci da tattalin arzikin jihar da ya durkushe
  • Daga cikin mambobin cibiyar AGEAC akwai Dr. Ngozi Okonjo-Iweala, Farfesa Ndubuisi Ekekwe da shi kansa gwamna Otti

Sani Hamza, kwararren edita ne a fanni n nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Jihar Abia - Gwamnan jihar Abia, Dr Alex Otti, ya nada mai girma Muhammadu Sanusi II, Dr. Ngozi Okonjo-Iweala (DG-WTO), da wasu a matsayin mambobin cibiyar tattalin arzikin jihar Abia.

Manufar cibiyar AGEAC ita ce taimakawa jihar Abia wajen zama cibiyar kasuwanci ta Afrika, Vanguard ta ruwaito.

Kara karanta wannan

"Mene Ka Ke Girkawa?" Fitaccen Na Hannun Daman Atiku Ya Ziyarci Buhari a Daura, Hotuna Sun Fito

Gwamnan Abia ya nada Sanusi II mukami mai muhimmanci
Gwamnan Abia ya nada Sanusi II mukami mai muhimmanci a gwamnatinsa. Hoto: @alexottiofr, @MSII_dynasty
Asali: Twitter

Yadda aka zabo mambobin cibiyar AGEAC

Gwamna Otti ya ce yana fatan zaratan mambobin cibiyar za su ba da shawarwarin da za su bunkasa kasuwanci, kudaden shiga da daga darajar jihar a Najeriya da Afrika baki daya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya kara da cewa cibiyar ta kunshi mutane 19 daga sassan Najeriya, wadanda ke da tarihin kwarewa a fannin kasuwanci da tattalin arziki.

Otti ya kuma ce akwai mutum biyar da aka saka a cibiyar da suka fito daga jihar Abia, da suka hada da shi kansa gwamnan, Mai shari'a, Ikechukwu Uwanna da Mr Kingsley Anosike.

Tattalin arziki ya durkushe a jihar Abia

Gwamnan ya koka kan yadda tattalin arzikin Abia ya durkushe saboda rikon sakainar kashi da gwamnatin baya ta yi, amma ya ce zai farfaɗo da tattalin jihar daga doguwar suma.

Ya ce:

Kara karanta wannan

Kwanaki 5 da hukuncin Kotun Koli, Sarakuna 4 sun ki taya Abba murnar galaba kan APC

"Tuni shirye-shiryen mu suka fara kawo babban sauyi na ci gaba a jihar Abia musamman ta fuskar tattalin arziki.
"Don haka ne ya zama dole mu samar da hanyoyi da za mu bunkasa kasuwanci da hanyoyin samun kudaden shiga da goyayya da sauran jihohi da kasashen duniya."

Aikin da mambobin cibiyar AGEAC za su yi

A cewar Otti, Mr Chinenye Mba-Uzoukwu, babban sakataren gwamnatin jihar, da Mr. Charles Egonye, mataimakin gwamnan da wasu mutum biyu ne za su tafiyar da sakatariyar cibiyar AGEAC.

ABN Tv ta ruwaito cewa Cibiyar AGEAC za ta kasance madaddalar ba da shawarwari na hanyoyin da jihar za ta bi don farfaɗo wa da bunkasa tattalin arzikin ta.

Mambobin cibiyar za su rinka aiki kafada da kafada da kwamishinonin jihar don magance matsalolin da ka iya tasowa a jihar da suka shafi kasuwanci da tattalin arziki.

Ga jerin sunayen mambobin cibiyar AGEAC:

  • Ms. Arunma Oteh, OON – Shugaba ta biyu
  • Mai girma Khaleefa Muhammad Sanusi II, CON, Shugaba na biyu
  • Mr. Bolaji Balogun – Shugaba na biyu
  • Mr. Victor Onyenkpa – Mamba
  • Mrs. Ifueko Omoigui Okauru, MFR – Mamba
  • Mr. Chidi Ajaegbu – Mamba
  • Mr. Uche Orji – Mamba
  • Mrs. Ndidi Nwuneli , MFR – Mamba
  • Mr. Chika Nwobi – Mamba
  • Dr. Olugbenga Adesida – Mamba
  • Prof. Ndubuisi Ekekwe – Mamba
  • Mazi Clement Owunna, MFR – Mamba
  • Dr. Uzodinma Iweala – Mamba
  • Mrs. Ezinwa Okoroafor – Mamba
  • Mr. George Agu – Mamba
  • Mazi Uzo Nwankwo – Mamba
  • Mr Chinedu Azodoh – Mamba
  • Dr. Ngozi Okonjo-Iweala, GCON – Babban mashawarci
  • Dr. Benedict Oramah, CON – Babban mashawarci

Kara karanta wannan

Tinubu, Shettima da gwamnoni sun dira Ibadan don taya Akande murnar cika shekera 85

Fasto ya nemi mabiyansa su ba shi albashinsu na watan Janairu

A wani labari mai ban al'ajabi, wani malamin coci, Fasto Anosike ya fada wa mabiyansa Ubangiji zai masu albarka idan suka bashi albashinsu na watan Janairu.

Fasto Anosike ya ce ma damar ba su samu albarkar Ubangiji nan da tsakiyar shekara ba, to zai mayar masu da kudin su.

Asali: Legit.ng

Online view pixel