Yan Bindiga Sun Kai Hari Kauyen Zariya, Sun Sace Uwa da Ɗanta, Mijin Ya Tsere

Yan Bindiga Sun Kai Hari Kauyen Zariya, Sun Sace Uwa da Ɗanta, Mijin Ya Tsere

  • Rahotanni sun bayyana cewa 'yan bindiga sun shiga wani kauyen karamar hukumar Sabon Gari da ke jihar Kaduna, sun sace uwa da ɗanta
  • A lokacin da suka 'yan bindigar suka kai farmakin, mijin matar ya tsere, amma ya bar matar da yaron mai suna Yusuf Bello
  • Yankin Zariya na ci gaba da fuskantar hare-haren 'yan bindiga, inda a ranar Litinin din da ta gabata aka kai hari kauyen Tumburku

Sani Hamza, kwararren edita ne a fanni n nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Jihar Kaduna - A ranar Laraba ne 'yan bindiga suka kai hari kauyen Doguwa da ke karamar hukumar Sabon Gari, jihar Kaduna, inda suka sace wata mata Halima da ɗanta Yusuf Bello.

Wani ganau ya shaida cewa mijin matar Mallam Bello, ya tsere yayin harin, amma 'yan bindigar sun tafi da matarsa da ɗansa Yusuf.

Kara karanta wannan

Bayan kashe Nabeeha, 'yan bindiga sun kuma kashe wata daliba, an samu karin bayani

Yan bindiga sun sace uwa da ɗanta a Zariya
Yan bindiga sun kai hari kauyen Zariya, sun sace uwa da ɗanta. Hoto: @PoliceNG
Asali: Twitter

Ko da jaridar The Guardian ta tuntubi kakakin rundunar 'yan sandan jihar Kaduna, ASP Mansir Hassan, ya tabbatarwa da faruwar lamarin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Matsalar tsaro: Mazauna yankin Zariya sun yi zanga-zanga

Wannan na zuwa ne bayan da mazauna garin Tumburku, wani kauyen karamar hukumar Giwa a jihar suka yi zanga-zanga kan yawaitar hare-haren 'yan bindiga a yankin.

Masu zanga-zagar sun isa har fadar Sarkin Zazzau don nuna bacin ransu kan yadda aka kyale 'yan bindigar suna cin karensu ba babbaka a yankunan Zariya.

Da yake jawabi ga manema labarai, jagoran masu zanga-zagar, Sani Danlami ya ce sun je fadar ne don mika kukansu ga Sarki Ahmed Nuhu Bamalli.

An kai hari kauyen Dogarawa a ranar Litinin

Ya ce suna da yakin cewa sarkin, wanda ya kasance uba mai sauraron koken jama'arsa, zai kai kukan su ga gwamnan jihar Uba Sani don daukar matakin gaggawa.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun tafka mummunar ɓarna, sun sace mata sama da 35 tare da kashe rayuka a arewa

The Cable ta ruwaito cewa 'yan bindiga sun kai hari kauyen Dogarawa a safiyar ranar Litinin din da ta gabata sai da 'yan bindiga suka kai harin garin.

Miyetti Allah ta kaddamar da kungiyar 'yan sa kai a Nasarawa

A wani labarin, kungiyar Fulani ta Miyetti Allah Kautal Haure, ta ba wasu mambobinta 1,144 horo tare da kaddamar da kungiyar 'yan sa kai a jihar Nasarawa.

A cewar shugaban kungiyar na kasa Abdullahi Bodejo, sun kafa kungiyar ne don taimakawa jami'an tsaro wajen magance matsalar 'yan bindiga, barayin shanu, masu garku a jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.