Takaitaccen tarihin sabon Sarkin Zazzau, Ambasada Ahmad Nuhu Bamalli

Takaitaccen tarihin sabon Sarkin Zazzau, Ambasada Ahmad Nuhu Bamalli

- Sabon Sarkin Zazzau, Ahmad Bamalli ya hau kujerar Sarki ya na shekara 54

- Ambasada Bamalli ya karanci ilmin shari’a a Digiri daga Jami’ar ABU Zariya

- Ya rike mukamai da dama a ma’aikatu, jihar Kaduna da gwamnatin Najeriya

A ranar 7 ga watan Oktoba, 2020, gwamnatin jihar Kaduna ta tabbatar da Ambasada Ahmad Nuhu Bamalli a matsayin sabon Sarkin Zazzau.

Legit.ng Hausa ta tsakuro kadan daga cikin tarihin sabon Sarkin, kamar yadda ya taba bada labarin kansa da kansa a lokacin ya na Jakada.

1. Haihuwa

An haifi Ahmad Nuhu Bamalli ne a birnin Zariya a ranar 8 ga watan Yunin 1966. Bayan wata guda da haihuwarsa Najeriya ta barke da yakin basasa.

2. Nasaba

Kakaninsa Malam Musa su ne su ka kafa sarautar kasar Zazzau bayan jihadin Shehu Danfodio. Mahaifinsa Magajin Gari, Nuhu Bamalli ya rasu ne a 2001 ya na shekara 84. A wurin mahaifinsa ne ya gaji sarautar Magajin Gari.

KU KARANTA: Yadda El-Ruai ya yi watsi da zaben takarar Sarkin Zazzau

Nuhu Bamalli ya na cikin manyan ‘yan siyasar farko a Arewa, kuma ya rike Ministan kasar waje.

3. Ilmin boko

Sabon sarkin ya yi karatun firamare da sakandare ne a Kaduna, daga nan ya tafi jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya, ya karanci ilmin shari’a. Daga baya Bamalli ya yi digirgir a fannin harkokin kasar waje. Bayan haka ya yi kwas a jami’o’in Harvard da Oxford da wasu makarantun a kasar waje.

4. Magajin Gari

A 2001 aka nada Ahmad Nuhu Bamalli a matsayin Magajin Gari ya na da shekara 35. Ambasada Bamalli bai cika zama a fada ba, amma a wasu lokuta ya kan gana da Marigayi Sarki Shehu Idris. Sabon Sarkin ya yi kwas-kwas na harkar shugabanci a manyan jami’o’in Duniya.

Takaitaccen tarihin sabon Sarkin Zazzau, Ambasada Ahmad Nuhu Bamalli
Ahmad Nuhu Bamalli Hoto: Twitter/Gov. Kaduna
Asali: Twitter

KU KARANTA: An cusa sunan Ahmad Bamalli cikin masu neman sarautar Zazzau

5. Aiki

Ambasada Bamalli ya fara aiki ne a banki, daga nan ya tafi ma’aikatar Nigerian Security Printing and Minting da ke buga kudi a Najeriya, a nan ya rike har kujerar babban Darekta.

6. Gwamnati

A 2015 aka zabi Ahmad Bamalli cikin wadanda za su yi wa sabuwar gwamnatin Nasir El-Rufai sharar fage. Bayan nan gwamnatin Kaduna ta nada shi Kwamishina na harkar zabe.

A shekarar 2016 aka zabi Nuhu Bamalli a matsayin Jakadan Najeriya zuwa kasar Thailand.

7. Tarihi

Mahaifinsa Nuhu Bamalli ya nemi sarautar Zazzau a 1975 amma bai yi nasara ba. Yanzu gidan Mallawa sun fito da Sarki, a karon farko bayan Alu dan Sidi da ya rasu a 1920.

Kwanakin baya Sanata Shehu Sani ya yi hasashe game da nadin sabon Sarkin Zazzau. ‘Dan siyasar ya nuna alamun da ke nuna cewa magajin Gari ne zai zama sabon Sarki.

A cewar Shehu Sani, daga Nahiyar Asiya Magajin Shehu Idris zai fito, kuma haka aka yi.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel