‘Yan Bindiga Sun Kai Farmaki Zaria, Sun Tasa Keyar Lakcara

‘Yan Bindiga Sun Kai Farmaki Zaria, Sun Tasa Keyar Lakcara

  • Gagararrun ‘yan bindiga sun kai mugun farmaki a Unguwar Kuregu da kuma Wusasa dake karamar hukumar Zaria a jihar Kaduna
  • An gano cewa ‘yan bindigan sun bayyana da tarin yawansu dauke da makamai kuma malamin kwalejin ilimi na tarayya 1 suka sace
  • Dagacin Wusasa, Injiniya Yusuf ya sanar da cewa ‘yan sanda sun kai musu taimako da gaggawa, lamarin da yasa ‘yan bindigan basu kwashi mutane da yawa ba

Zaria, Kaduna - ‘Yan ta’adda da aka fi zargin ‘yan bindiga sun kai farmaki tare da sace wani lakcara a kwalejin ilimi ta tarayya dake birnin Zazzau.

Zamfara ‘yan bindiga
‘Yan Bindiga Sun Kai Farmaki Zaria, Sun Tasa Keyar Lakcara. Hoto daga aminiyadailytrust.com
Asali: UGC

Miyagun ‘yan bindiga sun kai hari yankunan Unguwar Kuregu da Wusasa dake Zaria wurin karfe 11 na daren Litinin inda suka dinga barin wuta.

Dagacin Wusasa ya Magantu

A yayin tabbatar da aukuwar lamarin, Dagacin yankin Wusasa, Injiniya Isiyaku Dallami Yusuf, yace maharan masu tarin yawa ne suka kai harin a daidai lokacin da yawancin mutane suka kwanta barci.

Kara karanta wannan

Kaduna: An Tsinta Gawar ‘Yar Magajiya a Wani Otal dake Zaria, An Fara Bincike

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ya tabbatar da cewa ‘yan bindigan wadanda ke rike da miyagun makamai, baya ga taimakon jami’an tsaro da suka kai musu da gaggawa, da ta yuwu mutanen da zasu tasa keyarsu suna da yawa.

Injiniya ya kara da cewa, alamu na nuna cewa ba malamin kwalejin ilimin kadai suka zo garkuwa da shi ba saboda yawansu ya fallasa cewa akwai manufarsu babba da kuma tarin makaman da suka bayyana da su.

Dagaci ya yabawa ‘yan sanda

Ya jinjinawa jami’an tsaro da suka hanzarta zuwa tare da dakile harin kan lokaci bayan an nemi agajinsu.

Duk kokarin da aka dinga yi domin jin ta bakin mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna, Muhammad Jalige, ya faskara saboda bai dauka waya da aka dinga masa ba kafin rubuta wannan rahoton.

Kara karanta wannan

Daga Twitter: Matashi ya jefa kansa a matsala, ya shiga hannu bayan zagin Aisha Buhari

A zantawar da Legit.ng Hausa tayi da Hassana Muhammad, ma’aikaciyar jinya a asibitin Wusasa, ta bayyana cewa tabbas ‘yan bindigan sun kai farmaki yankin.

”’Yan bindiga sun kawo hari unguwar Kuregu da Wusasa kuma sun sace mutum daya. A daren Laraba suka shigo amma martanin gaggawa da ‘yan sanda suka yi ya taimaka matuka.
”Sai dai har yanzu ba a kama ko mutum daya cikinsu ba kuma ‘yan bindigan bamu samu labarin sun kira iyalan lakcaran da suka sace ba.”

- Muhammad mazauniya Unguwar Kuregu tace.

Yan bindiga sun kutsa ABU Zaria

A wani labari na daban, miyagun ‘yan bindiga sun kai farmaki a har cikin jami’ar Ahmadu Bello dake Zaria inda suka sace lakcara.

‘Yan bindigan sun sace Farfesa baki bayan farmakin da suka kai.

Asali: Legit.ng

Online view pixel