Ana Cikin Jimamin Kisan Nabeeha Yan Bindiga Sun Sace Daliban Jami'a a Katsina

Ana Cikin Jimamin Kisan Nabeeha Yan Bindiga Sun Sace Daliban Jami'a a Katsina

  • Wasu miyagun ƴan bindiga sun tafka savuwar ta'asa bayan sun yi awon gaba da wasu ɗalibai mata guda biyu na jami'ar Al-Qalam da ke Katsina
  • Ƴan bindigan sun sace ɗaliban ne waɗanda suka fito daga jihar Neja a lokacin da suke kan hanyarsu ta komawa makaranta
  • Shugaban ƙungiyar ɗaliban jihar Neja na ƙasa shi ne ya tabbatar da sace ɗaliban a cikin wata sanarwa da ya fitar

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Katsina - Wasu ƴan bindiga sun yi garkuwa da wasu ɗalibai mata biyu na jami’ar Al-Qalam da ke jihar Katsina.

Ɗaliban da aka sace waɗanda aka bayyana sunayensu a matsayin, Habiba Ango Shantali da Maryam Abubakar Musa, an yi garkuwa da su ne a hanyarsu ta komawa makaranta ranar Litinin, cewar rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya fadi hanya 1 da zai bi wajen magance matsalar rashin tsaro a Najeriya

Yan bindiga sun sace daliban jami'a a Katsina
Yan bindiga sun sace dalibai mata biyu na jami'ar Al-Qalam Hoto: @PoliceNG
Asali: Facebook

Shugaban ƙungiyar daliban jihar Neja na ƙasa, Kwamared Gambo Idris Shehu, ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun babban sakataren ƙungiyar, Kwamared Mohammed Ibrahim, rahoton National Daily ya tabbatar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wani ɓangare na sanarwar na cewa:

"Kwamitin zartaswa na ƙasa ya samu labari mai ban tausayi cewa, an yi garkuwa da wasu ɗalibanmu biyu daga jihar Neja da ke karatu a jami’ar Al-Qalam da ke Katsina, a hanyarsu ta komawa makaranta.
"Waɗanda abin ya shafa su ne Habiba Ango Shantali, ɗaliba ƴar 200L a sashin kimiyyar siyasa, da Maryam Abubakar Musa, ɗaliba 400L daga sashin nazarin kimiyyar ƙwayoyin halitta. Dukkansu sun fito ne daga ƙaramar hukumar Borgu."
"Allah ya kuɓutar da su daga hannun waɗannan miyagun mutanen."

Legit Hausa ta tuntuɓi kakakin rundunar ƴan sandan jihar Katsina, ASP Abubakar Sadiq, domin jin ta bakinsa kan sace ɗaliban, amma bai dawo da amsar saƙon da aka tura masa ba har zuwa lokacin kammala haɗa wannan rahoton.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya fusata kan matsalar rashin tsaro, ya sha sabon alwashi

Ƴan bindiga sun kashe Nabeeha

Wasu miyagun ƴan bindiga sun halaka Nabeeha Al-Kadriyar wacce suka yi garkuwa da ita tare da ƴan uwanta da mahaifinsu a birnin tarayya Abuja.

Ƴan bindigan sun halaka Nabeeha ne bayan da aka gaza kai kuɗaɗen fansar sa suka nema domin a sako su.

Ƴan Bindiga Sun Kai Farmaki Sansanin Sojoji

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu miyagun ƴan bindiga sun kai farmaki a wani sansanin sojoji da ke jihar Katsina.

Duk da sojoji sun yi nasarar daƙile harin, ƴan bindigan sun lalata wasu motoci da kayayyaki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel