Digirin Bogi: ICPC Ta Yi Zama da Dan Jaridar, Ta Dauki Mummunan Mataki Kan Lamarin

Digirin Bogi: ICPC Ta Yi Zama da Dan Jaridar, Ta Dauki Mummunan Mataki Kan Lamarin

  • Musa Aliyu, shugaban Hukumar ICPC ya gana da dan jaridar Daily Nigerian kan badakalar da ya bankado a Benin
  • Umar Audu da ke aiki a Daily Nigerian ya yi nasarar mallakar satifiket a cikin makwanni shida kacal ba tare da halartar Jami'ar ba
  • Legit Hausa ta ji ta bakin wasu daliban da ke karatu a jami'oin Najeriya kan wannan lamari da ya faru

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Shugaban Hukumar Yaki da Cin Hanci ta ICPC, Musa Aliyu ya gana da dan jaridar Daily Nigerian kan badakalar digiri a Benin da Togo.

Don samun ingantaccen labari game da lamarin, shugaban ya yi ganawar ce da Umar Audu don gujewa jita-jita.

Kara karanta wannan

NSCDC ta kama fasto da wasu mutane biyu kan damfara a Kogi

Hukumar ICPC ta gayyaci dan jarida kan badakalar digiri a Benin
Hukumar ICPC ta fara bincike kan badakalar digiri a Benin. Hoto: @icpcnigeria.
Asali: Twitter

Mene ICPC ke cewa kan badakalar digiri?

Kakakin hukumar, Azuka Oguagua shi ya bayyana haka a yau Laraba 3 ga watan Janairu a Abuja.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce ganawar ta gudana ne a hedkwatar hukumar da ke birnin Abuja a yau Laraba.

A ranar 30 ga watan Disamba, jaridar Daily Nigerian ta bankado yadda wasu jami'an gwamnati ke taimakawa a harkar samun satifiket din digiri na bogi.

Rahoton ya bayyana yadda Umar Audu ya kammala digiri a cikin sati shida a Jami'ar Ecole Superieure de Gestion et de Technologies, ESGT a Cotonou da ke kasar Benin.

Ta yaya dan jaridar ya samu satifiket?

Audu ya samu satifiket din ba tare da nema ko zuwa makaranta ba, inda ya kammala ba tare da rubuta jarrabawa ba.

Duk da cewa bai taba zuwa kasar ba, amma jami'an shige da fice daga Najeriya da Benin sun taimaka masa da takardum shaidar cewa ya fita.

Kara karanta wannan

Tashin hankali bayan tirela ta murkushe sabon dan sanda a bakin aiki a jihar Arewa, bayanai sun fito

Legit Hausa ta ji ta bakin wasu dalibai kan lamarin:

Abubakar Yusuf da ke tsangayar kimiyyar tattalin arziki a Jami'ar jihar Gombe ya ce gaskiya wannan abin bakin ciki ne yadda ilimi ke kara tabarbarewa a kasar.

Aisha Hussaini Muhammad ita ma a Jami'ar ta ce:

"Babban damuwa ta yadda muke bata shekaru hudu zuwa biyar amma wai wani ya samu satifiket a kasa da watanni biyu.

Muhammad Shehu da ke tsangayar kimiyyar siyasa a Jami'ar Kashere ya ce matakin da Tinubu ya dauka ya yi dai-dai wanda hakan zai zama izina ga saura.

Dan Najeriya ya kammala digiri a sati 6

A wani labarin, jaridar Daily Nigerian ta bankado yadda ake mallakar takardar digiri a cikin sati shida kacal.

Wani dan jarida, Umar Audu ya yi shigar bultu inda ya nemi mallakar satifiket din ta hanyar ba da cin hanci da rashawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel