Dilallan Man Fetur Sun Sake Magana Kan Farashin Mai da Matakin NNPCL Na Karshe

Dilallan Man Fetur Sun Sake Magana Kan Farashin Mai da Matakin NNPCL Na Karshe

  • ‘Yan kasuwar man fetur sun sake fitowa domin jaddada matsayarsu dangane da shirin kara farashin man fetur da ake yayatawa
  • ‘Yan kasuwan sun kuma lura cewa, kayyade farashin man fetur a Najeriya ya rataya ne a kan kamfanin man fetur na kasa (NNPC)
  • Farashin man fetur a halin yanzu yana tsakanin naira 580 zuwa naira 650, ya danganta da inda masu ababen hawa suke

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Kungiyar dillalan man fetur mai zaman kanta ta Najeriya (IPMAN) ta sake nanata cewa babu wani shiri na kara kudin man fetur, sabanin labaran da ake yayatawa.

A wata sanarwa a ranar Litinin, ‘yan kasuwar sun ce kamfanin mai na NNPCL ya kasance shi kadai ne mai shigo da fetur kuma shi kadai ne zai iya kayyade farashin fetur din.

Kara karanta wannan

Tattalin Arziki: Za a kori dinbin mutane daga wuraren aiki a dalilin karyewar Naira

Ba za a kara farashin man fetur ba
Ba hurumin mu ba ne: Dillalan man fetur sun fadi matsayarsu kan karin kudin mai
Asali: Getty Images

‘Yan kasuwar sun kuma bayyana cewa kamfanin na NNPC na iya samun koma baya a farashin man fetur saboda yadda yake da hannu wajen sayar da danyen mai.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Babu batun karin farashin man fetur a yanzu

Jaridar Independent ta ruwaito Ukadike Chinedu, kakakin kungiyar IPMAN ya bayyana cewa sauran ‘yan kasuwa masu lasisi sun daina shigo da man fetur saboda wasu manyan dalilai.

Kungiyar IPMAN ta bukaci jama’a da kada su damu da tsadar man fetur domin kamfanin NNPC na iya ci gaba da samar da man fetur a farashin yanzu, inji rahoton Punch.

A baya bayan nan ne dai rahotanni suka rinka yawo a kafofin sada zumunta inda ake hasashen kungiyar IPMAN za ta kara kudin litar fetur zuwa naira 1,200.

2024: Najeriya ta koma ta 22 a kasashe masu arahar man fetur a duniya

Kara karanta wannan

Kwararru sun bayyana dalilai 5 da suka sa yara ke shan wahala a darasin lissafi a makaranta

Legit Hausa a ranar Litinin ta kawo rahoton yadda Najeriya ta koma ta 22 a jerin kasashen duniya da suke sayar da man fetur a farashi mai araha.

A mafi yawan kasashen duniya, ana sayar da litar man fetur sama da naira 1,500, amma akwai kasashen da kudin litar bai kai hakan ba, kamar dai kasar Iran.

Kasar Hong Kong ce mafi tsada a farashin man fetur inda kowace lita ake siyar da ita kan $3.101 (watakan naira 2,835. Birnin na daga garuruwan da suka fi ko ina tsadar rayuwa a duniya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Online view pixel