Kwararru Sun Bayyana Dalilai 5 da Suka Sa Yara Ke Shan Wahala a Darasin Lissafi a Makaranta

Kwararru Sun Bayyana Dalilai 5 da Suka Sa Yara Ke Shan Wahala a Darasin Lissafi a Makaranta

  • Wasu kwararru a fannin ilimi sun bayyana mahangarsu kan dalilan da suka sa yara ba sa iya karatu da lissafi a Najeriya
  • Wannan na zuwa bayan sakataren gwamnatin jihar Enugu, Farfesa Onyia ya ce kashi 50% na yaran yankin ba sa iya karatu da lissafi
  • Jaridar Legit ta tattauna da wasu kwararru a fannin ilimi don jin ta bakin su kan wannan lamari

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

An sami sa in sa a kwanan nan kan furucin sakataren gwamnatin jihar Enugu, Farfesa Chidiebere Onyia, da ya ce kashi 50% na yara a yankin ba sa iya warware matsalar lissafi a makaranta.

Ya bayyana hakan a wani taron kungiyar tsaffin daliban makarantun sakandire a Awkunnanaw, Enugu, inda ya gabatar da wata makala ga mahalarta taron.

Kara karanta wannan

Bayan cewa bai son a kai masa ziyara, Buhari ya yi kyautar galleliyar mota ga dan a mutunsa

Dalibai ba sa gane darasin lissafi a makaranta
Kwararru sun bayyana dalilai 5 da suka sa yara ke shan wahala a darasin lissafi a makaranta. Hoto: Olukayode Jaiyeola/Pius Utomi Ekpei
Asali: Getty Images

Kwararru sun magantu kan dakushewar kwakwalwar yara a makarantu

Farfesa Onyia ya ce:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Bincike ya nuna bayan shafe shekaru shida a firamare, kaso 50% na yaran ba sa iya warware karamin lissafi, kuma ba sa iya karanta kalma ɗaya ta turanci."

A wannan nan gabar, jaridar Legit ta tuntubi wani kwararre a fannin ilimi, Dr. Babatunde Oyinade wanda ya taba koyarwa a jami'o'i tara da kwaleji biyu a Amurka.

Haka zalika, jaridar ta zanta da Auwal Musa Rafsanjani, shugaban kwamitin gudanarwa na kungiyar Amnesty ta kasa-da-kasa reshen Najeriya.

Dalilai biyar da suka kawo nakasu ga ilimin yara a Najeriya

1. Matsin lamba daga iyaye

Dr. Oyinade ya ce matsin lamba daga iyaye na tilasta yara zuwa makaranta ba tare da sun fara fahimtar wasu dabaru na yin karatu ba.

Ya yi nuni da cewa, akwai iyaye masu tilasta yaro yin karatu ko da kwakwalwarsa ba ta shirya ba, da kuma yi masa tsallaken aji don ya kammala karatu da wuri.

Kara karanta wannan

Don burge Bankin Duniya: An tona asirin dalilin Tinubu na kara farashin mai da wutar lantarki

2. Yawan dalibai da karancin malamai a makarantu

Ya bayyana cewa a Amurka, za ka taras akwai dai daito na yawan dalibai da malamai, sabanin Najeriya da za ka ga daruruwan dalibai amma malamai 'yan kadan.

Dr. Oyinade ya ce malami kan gaza koyar da yara saboda yawansu, daliban kuma ba za su iya gane komai ba. Yawan dalibai a aji daya na tauye ilimin yara.

3. Rashin biyan albashi mai tsoka ga malamai

Ya kuma kara yin nuni da cewa rashin wadataccen albashi na haifar da nakasu ga koyarwar malamai, saboda ba su da karsashi ko kwarin guiwar ba da ilimin.

Kwararren ya ce malamai kan dauki halin ko in kula ga abin da yaran ke koya, ko sun gane ko ba su gane ba, ba zai dami malaman ba tunda ba a biyan su albashi mai kyau.

4. Rashin kwararrun malamai a makarantun yara

Dr. Oyinade ya kuma diga ayar tambaya kan kwarewar malaman da gwamnati ke dauka aikin koyarwa a makarantun firamare na gwamnati.

Kara karanta wannan

Allahu Akbar: Mutum uku da aka sace sun mutu a kokarin gudowa daga hannun yan bindiga

Ya ce mallakar kwalin digiri ba shi ne zai ba mutum damar koyarwa ba a nasa hangen, wanda ya karanci koyarwa ne kawai ya kamata ya koyar.

5. Cin hanci da rashawa

Shi kuwa Auwal Rafsanjani ya zargi cin hanci da rashawa tsakanin manyan kasar da zama silar lalacewar ilimi a Najeriya.

Ya bayyana cewar 'yan siyasa na sace kudin kasar don tura 'yayansu karatu kasar waje, hakan ke saka makarantun cikin gida su lalace ba tare da sun damu ba.

Rafsanjani ya ce gina makarantun kudi da 'yan siyasar ke yi da kudin jama'a ya durkusar da ingancin makarantun gwamnati a kasar.

"Allah ne kawai zai biya malamai ba wai iyaye ko gwamnati ba"

Wani malamin makarantar firamare a garin Funtua, Mallam Nura Lawal Mailafiya, ya ce hidimar koyar da yara karatu sai dai Allah ya biya malamai kawai.

A cewarsa:

"Makarantun kudi suna biyan malamai naira dubu 15 a wata, wasu wuraren ma har naira dubu 10 zuwa 13 suna biya, sai idan makarantar na da tsada za a biya naira dubu 20 zuwa 30.

Kara karanta wannan

Bayin Allah sama da 100 sun mutu yayin da bama-bamai suka tashi a wurin taro kusa da Masallaci

"Nawa mutum zai kashe a kudin mashin, nawa zai kashe na siyan abinci, idan yana da iyali ya zai yi da cefane? Kawai sai dai mu nemi lada wajen Allah, amma ba wajen makaranta ko gwamnati ba."

Ya nuna takaicinsa kan yadda da yawan makarantu ke fifita jin dadin dalibai amma su watsar da jin dadin malamai, inda ya ce sai malami ya samu nutsuwa ne zai ji karkashin koyarwa.

Kungiyar NANS ta Benin ta nemi a kama dan jarida Umar Audu

A wani labarin, Kungiyar daliban Najeriya da ke karatu a jamhuriyyar Benin ta nemi a kama dan jaridar da ya fitar da rahoton 'digiri dan Kwatano', Umar Audu.

A cewar shugaban kungiyar Ugochukwu Favour, wannan binciken zai goga kashin kaji ga gwamnati, hukumar NYSC da hukumar shige da fice ta Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel