Digirin Bogi Na Kwatano: Ban Taba Shiga Aji Ba N600k Kacal Na Kashe, Dan Jarida

Digirin Bogi Na Kwatano: Ban Taba Shiga Aji Ba N600k Kacal Na Kashe, Dan Jarida

  • Ɗan jaridar da ya yi binciken ƙwaƙwaf kan yadda ake samun kwalin digiri cikin sati shida ya yi ƙarin haske kan yadda ya samu na shi kwalin
  • Umar Audu ya bayyana cewa duka abin da ya kashe har kwalin digirin ya zo hannunsa ba wuce N600k ba
  • Ya yi nuni da cewa bai taɓa zuwa makarantar ba ballantana ya zana jarabawa kuma har ofis aka kawo masa kwalin digirin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kano - Umar Shehu Audu ɗan jaridar da ya bankaɗo hanyar samun digirin bogi na Kwatano, ya yi ƙarin haske kan hanyoyin da yabi ya samu kwalin digirin.

Umar Audu wanda yake aiki da jaridar Daily Nigerian ya dai bi wasu hanyoyi inda ya samu kwalin digiri daga wata jami'a a Jamhuriyar Benin, ba tare da ya taɓa shiga aji ba.

Kara karanta wannan

Gwamna Fubara ya bayyana dalili 1 da yasa ya amince da yin sulhu a rikicinsa da Wike

Umar Audu ya fadi kudin da ya kashe wajen samun digiri
Umar Shehu ya ce N600k kawai ya kashe wajen samun digiri a Kwatano Hoto: @Theumar_audu
Asali: Twitter

Wannan tonon sililin da ɗan jaridar mai bincike ya yi, ya sanya gwamnatin tarayya ta dakatar da tantancewa da amincewa da kwalin digiri daga ƙasashen Jamhuriyar Benin da Togo.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ta wacce hanya ya samu kwalin digirin?

Audu ya samu satifiket ɗin digirin daga jami'ar Ecole Superieure de Gestion et de Technologies, ESGT a Cotonou da ke Jamhuriyar Benin, ba tare da an ba shi takardar ɗauka ba, ko ya taka ƙafa zuwa harabar jami'ar.

A yayin wata hira da Channels tv ya bayyana cewa har kwalin digirinsa ya zo hannunsa cikin sati shida, bai taɓa zuwa makarantar ba, ballantana har ya shiga aji ko ya zana jarabawa.

Ya bayyana cewa N600k kawai ya kashe inda aka kawo masa kwalin digirinsa har ofis bayan ya bi ta hannun wani mutum da yake harkar smaar da digirin na bogi.

Kara karanta wannan

Cikakken jerin jami'o'in kasashen waje da gwamnatin Tinubu ta haramta a Najeriya

FG ta dakatar da karɓar digiri daga Togo da Benin

Gwamnatin tarayya ta ɗauki matakin dakatar da tantancewa da amfani da takardun shaidar kammala digiri daga ƙasashen Jamhuriyar Benin da Togo.

Gwamnatin ta cimma wannan matakin ne wani rahoto ya yi bayani dalla-dalla kan yadda ake samun kwalin digiri a wata jami’a a Jamhuriyar Benin cikin sati shida kacal.

ICPC Ta Gayyaci Umar Audu

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban hukumar ICPC ya samu zama da Umar Shehu Audu, ɗan jaridar da ya yi fallasa kan yadda ake samun kwalin digiri cikin sati shida a Jamhuriyar Benin.

Shugaban hukumar ya gana da ɗan jaridar ne domin samun cikakken bayani kan yadda ake cin wannan kasuwa ta digirin bogi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel