Hukumar EFCC Za Ta Yi Wa Sadiya Farouk Tambayoyi Kan Zargin Karkatar da N37bn a Gwamnatin Buhari

Hukumar EFCC Za Ta Yi Wa Sadiya Farouk Tambayoyi Kan Zargin Karkatar da N37bn a Gwamnatin Buhari

  • Hukumar hana yi wa tattalin arziƙinƙasa ta'annati (EFCC) za ta yi wa Sadiya Umar Farouk tambayoyi
  • Hukumar za ta tambayi tsohuwar ministar ne kan zargin karkatar da N37bn daga ma'aikatar jinƙai a lokacin da take minista
  • Tuni dai hukumar ta aike da katin gayyata ga Sadiya wacce ta yi aiki a gwamnatin tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Ana sa ran hukumar yaƙi da yi wa tattalin arzikin ƙasa ta'annati (EFCC) za ta yi wa tsohuwar ministar harkokin jin ƙai, Sadiya Umar-Farouk tambayoyi kan badaƙalar N37.1bn.

Wata majiya mai ƙarfi ta EFCC ta tabbatar da hakan ga Channels tv a wata tattaunawa ta wayar tarho a ranar Laraba, 2 ga watan Janairu.

Kara karanta wannan

Hukumar EFCC ta cafke Halima Shehu shugabar hukumar NSIPA bayan Shugaba Tinubu ya dakatar da ita

EFCC za ta yi wa Sadiya Farouk tambayoyi
Tsohuwar minista Sadiya Farouk za ta amsa tambayoyi a wajen EFCC Hoto: Sadiya Umar Farouq CON
Asali: Twitter

Sadiya ta riƙe muƙamin minista a lokacin tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari daga watan Agustan 2019 zuwa ranar 29 ga watan Mayun 2023.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A makon da ya gabata ne hukumar EFCC ta gayyaci tsohuwar ministar bayan wani bincike da aka gudanar kan ayyukanta a ma’aikatar a lokacin da ta rike madafun iko, cewar rahoton Daily Trust.

Wane bincike EFCC ke yi kan Sadiya?

Ana binciken ta ne kan zunzurutun kuɗi har N37.1bn da ake zargin an wawure a ƙarƙashin kulawarta ta hannun wani ɗan kwangila, James Okwete.

Hukumar ta buƙaci tsohuwar ministar ta bayyana a gaban masu bincike a hedikwatar ta da ke Jabi, Abuja, da ƙarfe 10:00 na safiyar yau Laraba.

Sai dai, majiyar wacce ta nemi a sakaya sunanta ta ce har yanzu tsohuwar ministar ba ta bayyana a hedikwatar EFCC ba.

Kara karanta wannan

Cikakken jerin jami'o'in kasashen waje da gwamnatin Tinubu ta haramta a Najeriya

A cewar majiyar, an kuma gayyaci wasu jami’an da suka yi aiki da ita domin su ba da ƙarin haske kan yadda al’amuran ma’aikatar suka kasance cikin shekara huɗu da suka gabata.

Sadiya Ta Yi Martani Kan Zargin Karkatar da N37bn

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohuwar ministan jin ƙai, Sadiya Umar Farouk ta nesanta kanta daga zargin karkatar da N37bn ta hannun wani ɗan kwangila, James Okete.

Tsohuwar ministar ta nesanta kanta da sanin ɗan kwangilar, inda ta yi barazanar ɗaukar matakin shari'a kan masu shirin ɓata mata suna.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel