Bayan Dan Jarida Ya Yi Fallasa, FG Ta Dakatar Da ‘Karbar’ Digiri Daga Togo da Jamhuriyar Benin

Bayan Dan Jarida Ya Yi Fallasa, FG Ta Dakatar Da ‘Karbar’ Digiri Daga Togo da Jamhuriyar Benin

  • Gwamnati ta dauki matakin dakatar da amfani da takardun digiri da suka fito daga makarantun jamhuriyyar Benin da Togo
  • Gwamnati ta dauki matakin ne biyo bayan wani rahoto da ya nuna dalibai na samun takardun digirin a kasa da watanni biyu daga kasashen
  • Da wannan kuma gwamnati ta kafa wani kwamiti da zai yi bincike, wanda ya shafi hukumar DSS, NYSC da hukumar harkokin kasar waje

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja - Gwamnatin tarayya ta dakatar da tantancewa da amfani da takardun shaidar digiri daga jamhuriyar Benin da Togo.

Wannan matakin ya biyo bayan wani rahoto da ya yi bayani dalla-dalla yadda ake samu digiri a wata jami’a a Jamhuriyar Benin cikin kasa da watanni biyu.

Kara karanta wannan

Mataimakin shugaban majalisar dattawa ya raba motoci 60 a jihar Kano, ya faɗi muhimmin dalili 1

Gwamnatin Najeriya ta wofantar da kwalin digiri na makarantun jamhuriyar Benin da Togo
Gwamnatin Najeriya ta wofantar da kwalin digiri na makarantun jamhuriyar Benin da Togo
Asali: Getty Images

Bayanin hakan na kunshe a wata sanarwa da aka fitar a ranar Talata, daga Augustina Obilor-Duru a madadin daraktan yada labarai da hulda da jama’a na ma’aikatar ilimi ta tarayya, rahoton Leadership.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnati za ta gudanar da bincike

Gwamnatin tarayya ta koka da cewa:

"Wasu 'yan Najeriya na amfani da munanan hanyoyin da ba su dace ba don samun digiri tare da neman samun guraben aikin yi wadanda ba su cancanta ba."

Gwamnatin ta ce dakatarwar za ta ci gaba da kasancewa har sai an kammala binciken da ya shafi ma'aikatun harkokin waje da ilimi na Najeriya da na kasashen biyu da kuma hukumar tsaro ta DSS, da hukumar yi wa kasa hidima (NYSC).

Channels TV ta ruwaito ma’aikatar na yin kira ga jama’a da su ba da goyon wajen samar da bayanai masu amfani da za su taimaka wajen samar da mafita mai dorewa domin hana afkuwar lamarin.

Kara karanta wannan

"Lallai bai da kunya": An fallasa wani dattijo bayan ya aikewa budurwa sakonnin da basu dace ba

Mutum 6 sun mutu a wani hatsarin mota kan titin Kaduna-Zariya

A wani labarin na daban, wani hatsarin mota da ya afku a safiyar Talata a hanyar Kaduna zuwa Zariya ya yi ajalin mutum 6 yayin da 11 suka jikkata.

Hukumar kiyaye haddura ta kasa reshen jihar Kaduna ta tabbatar da faruwar hatsarin, inda ta ce direbobin da ba 'yan asalin jihar Kaduna ba ne ke haddasa hatsari a titin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Online view pixel