Gwamnatin Kaduna ta garkame bankuna guda 3 saboda kin biyan haraji

Gwamnatin Kaduna ta garkame bankuna guda 3 saboda kin biyan haraji

Hukumar tattara haraji ta jahar Kaduna, KADIRS, ta garkame rassa guda uku na bankin First City Monument da Keyston Bank dake cikin garin jahar Kaduna saboda kama su da laifin kin biyan haraji ga gwamnati.

Daily Trust ta ruwaito rassan bankunan da jami’an hukumar KADIRS suka kulle sun hada da na unguwar Sabon Tasha, titin Ali Akilu, titin Bank Road da kuma na titin Yakubu Gowon, inda hukumar ta bayyana bankuna a matsayin masu taurin bashin biyan kudin haraji.

KU KARANTA: Gwamnatin Ganduje ta garkame wani babban banki saboda bashin N423m

Gwamnatin Kaduna ta garkame bankuna guda 3 saboda kin biyan haraji
Gwamnatin Kaduna ta garkame bankuna guda 3 saboda kin biyan haraji
Asali: Facebook

Rahotanni sun tabbatar da cewa gwamnatin jahar Kaduna na bin bankin FCMB bashin kudi naira miliyan 72, yayin da take bin bankin Keyston zambar kudin haraji naira miliyan 220.

Idan za’a tuna a kwanakin baya ma gwamnatin jahar Kano ta garkame bankunan Zenith Bank guda uku dake jahar Kano saboda nokewa wajen biyan harajin kudaden shiga da suka kai zambar kudi naira miliyan 423.

Majiyarmu ta ruwaito hukumar tattara haraji ta jahar Kano ce ta gudanar da wannan aikin garkame bankunan dake kan hanyar Murtala Muhammad, Bello road da kuma titin gidan Zoo.

A wani labarin kuma, mai martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sunusi II ya yi maraba da ziyarar aiki na yini daya da mataimakin shugabankasa Farfesa Yemi Osinbajo ya kai jahar Kano a ranar Litinin, 13 ga watan Janairu.

Sarkin ya bayyana haka ne yayin da Osinbajo ya kai masa gaisuwar ban girma a fadarsa dake cikin birnin Kano, inda yace Osinbajo ya dauki jahar Kano tamkar gidansa, don haka a kullum suna maraba da zuwansa.

Osinbajo ya kai ziyarar ne domin kaddamar da wasu manyan ayyuka guda biyu da gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje ta aiwatar da suka hada da gadar sama ta Alhassan Dantata dake Sabon Gari da kuma gadar Tijjani Hashim dake kofar Ruwa.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel