Tinubu Ya Dawo Da Shirin Ciyar Da Yan Makaranta Abinci Kyauta Da Gwamnatin Buhari Ta Fara

Tinubu Ya Dawo Da Shirin Ciyar Da Yan Makaranta Abinci Kyauta Da Gwamnatin Buhari Ta Fara

  • Gwamnatin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ta sake dawo da shirin ciyar da dalibai da gwamnatin tshon shugaba Buhari ta kawo
  • Shugaba Tinubu ya ce ya dawo da shirin don bunkasa harkar koyo da koyarwa a kananan makarantu don rage yawan yara masa zuwa makaranta
  • Haka zalika, gwamnati ta cire shirin daga ma'aikatar jin kai zuwa ma'aikatar ilimi don ganin ya samu muhimmiyar kulawar da ya ke bukata

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja - Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ba da umurnin dawo da shirin ciyar da dalibai domin magance yawan daliban da ke gararamba a garuruwan Najeriya.

Gwamnatin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ne ya fara kawo shirin ciyarwar amma ya dakatar da shi bayan dogon lokacin da aka dauka ana yin sa.

Kara karanta wannan

Jerin garuruwan da matafiya za su samu ragin 50% da zababbun kamfanonin sufuri da ke cikin tsarin

Tinubu ya dawo da shirin ciyar da dalibai abinci
Tinubu ya dawo da shirin ciyar da yan makaranta abinci kyauta da gwamnatin Buhari ta fara. Hoto: @officialABAT, @NHGSFP
Asali: Twitter

Ma'aikatar Ilimi za ta ja ragamar shirin ciyar da dalibai abinci

Amma yanzu da Tinubu ya dawo da shirin, ya ce zai taimaka wajen magance duk matsalolin da ake samu wajen ba da ilimi ga dalibai daga matakin farko, Daily Trust ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban kasar ya bayyana hakan ta bakin ministan ilimi Farfesa Tahir Mamman a wani taron bita na kwana daya da aka gudanar a Abuja, inda ya ce shirin zai dawo da yara makaranta.

A cewar ministan, shugaban kasa ya ba da umurnin a cire shirin ciyarwar daga ma'aikatar jin kai a mayar da shi karkashin ma'aikatar ilimi.

Ministan ya kuma ce manufar taron shi ne samar da hanyar da za a tabbatar da an aiwatar da duk wasu tsare-tsare da za su bunkasa harkar koyo da koyarwa tun daga kananun makarantu.

Kara karanta wannan

Kyakkyawar budurwa ta fashe da kuka bayan samun kyautar N20k don ta biya kudin makaranta

Wakilin Dalibai: Muna rokon Tinubu ya mayar da ilimi ya zama kyauta

A wani labarin, Wakilin Daliban Durbin Katsina, Sanusi Yau Mani ya yi kira ga Shugaba Tinubu da ya ba hukumar JAMB umurnin janye batun karin kudin jarrabawar UTME 2024.

Wakilin Daliban wanda ya zanta da Legit Hausa inda ya ce ya kamata ilimi ya zama kyauta a Najeriya kamar yadda aka yi shi a shekarun baya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.