Karancin Kudi: CBN Ya Bayyana Dalili Daya Tak da Ke Jawo Matsalar a Najeriya, Ya Fadi Mafita

Karancin Kudi: CBN Ya Bayyana Dalili Daya Tak da Ke Jawo Matsalar a Najeriya, Ya Fadi Mafita

  • Babban Bankin Najeriya, CBN ya bayyana dalilin da ya sa ake samun karancin kudade a wasu yankuna na kasar
  • Daraktan yada labarai na bankin, AbdulMumin Isa shi ya bayyana dalilin karancin kudin a yau Alhamis 2 a watan Nuwamba a Abuja
  • Isa ya ce wannan matsala ba ta rasa nasaba da makudan kudade da mutane su ke cire wa ba kakkautawa

Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja – Babban Bankin Najeriya, CBN ya bayyana cewa akwai isassun kudade na gudanar da kasuwanci a kasar a halin yanzu.

Wannan sanarwar na zuwa ne yayin da aka fara korafe-korafen samun karancin kudade a wasu jihohi a Najeriya, cewar Channels TV.

Kara karanta wannan

'Ina da tabbaci: CBN ya dauki mataki daya tak da zai inganta naira, za ta dawo kasa da dubu 1

CBN ya fadi dalilin da ya jawo karanci kudi
CBN ya yi martani kan karancin kudi a kasar. Hoto: CBN.
Asali: Twitter

Wane sanarwa CBN ta fitar kan karancin kudi?

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da daraktan yada labarai, AbdulMumin Isa ya fitar a yammacin yau Alhamis 2 ga watan Nuwamba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Isa ya ce matsalar karancin kudaden da ake samu ya faru ne sakamakon yawan cire makudan kudade da mutane ke yi a kwanakin nan, cewar TheCable.

Ya ce hakan ya jawo bankunan sun fara rasa kudade musamman a injunan cire kudade na ATM a fadin kasar.

Har ila yau, ya ce mutanen Najeriya sun tsorata da maganar karancin kudaden wanda ya saka kowa ke zuwa cire wa don gudun shiga matsala

Legit ta ji ta bakin wasu kan sanarwar CBN:

Lawan Abdullahi ya ce a gaskiya wannan ba hujja ba ne, ta yaya za a yi mutum da kudinshi ace kada ya cire.

Kara karanta wannan

Shugaban NLC ya magantu kan yadda aka lakada masa duka a jihar Imo

Nasiru Ibrahim ya ce:

"Ku ne sanadin tashin dalar ai wanda ya saka komai ya yi tsada a kasar yadda talaka zai sha wahala."

Yusuf Abubakar ya ce idan har hakan zai kara darajar dala ai abin a yaba ne.

An fara wahalar kudi a Najeriya

A wani labarin, an bayyana 31 ga Disamba a matsayin ranar da za a daina karbar tsoffin kudade a Najeriya.

Kotun koli ta tabbatar da haka inda ta ce za a daina karbar tsoffin Naira 200 da 500 da 1000.

Tun kafin wa'adin ya zo, 'yan Najeriya sun fara kokawa kan yadda aka fara wahalar kudaden kamar yadda aka yi a baya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel