Tattalin Arziƙi: Za a Ƙara Cin Wahala, Masani Ya Yi Hasashen Shekarar Samun Sauƙi

Tattalin Arziƙi: Za a Ƙara Cin Wahala, Masani Ya Yi Hasashen Shekarar Samun Sauƙi

  • A ra’ayin Bismarck Rewane, sauki ba zai zo wa mutanen Najeriya nan da ‘yan makonni kadan ba
  • Masanin tattalin arzikin ya nuna za a kai akalla watannin farkon 2024 kafin abubuwa su daidaita
  • Rewane ya yi magana kan tasirin tsare-tsaren da Bola Tinubu ya kawo bayan ya karbi mulki a Mayu

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Abuja - Bismarck Rewane fitaccen masanin harkar tattalin arziki ne a Najeriya, ya ce ana sa ran a samu cigaba daga farkon shekarar 2024.

Da aka yi hira da shi a tashar Arise TV a ranar Asabar, Mista Bismarck Rewane ya nuna mutanen Najeriya za su cigaba da fama da wahala.

Masanin ya shaida cewa sai zuwa watannin farkon shekara mai zuwa ne abubuwa za su soma lafawa, tattalin arzikin kasar zai fara zabura.

Kara karanta wannan

A Kurarren Lokaci, Tinubu Ya Cire Mutum 4 a Jerin Wadanda Za A Ba Kujerar Minista

Bola Tinubu
Bola Tinubu ya gaji Muhammadu Buhari Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Sai farkon shekara mai zuwa

Shugaban kamfanin na Financial Derivatives ya nuna da farko ya na zaton matsin lamban ba zai dade ba, amma yanzu yana ganin akwai aiki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Mummunan labarin shi ne za a shiga cikin wahala, za a samu karin kunci na gajeren lokaci, amma labari mai dadi shi ne za a samu cigaba a farkon 2024.
A baya ina tunanin za mu samu sauki da wuri, amma dole sai an gabatar da karin kasafin kudi, kuma kudi ya fara yawo a cikin al’umma tukuna."

- Bismarck Rewane

Tinubu ya na bukatar shawarwari

Gwamnati ta janye tallafin man fetur, hakan ya jawo karin tsadar rayuwa a Najeriya. Rewane ya ce sai kyau a ba Bola Tinubu shawara da kyau.

A game da daidaita kudin kasashen waje da bankin CBN ya yi, Rewane ya nuna sai an yi kokarin magance tsadar kaya da tashin farashi a kasuwa.

Kara karanta wannan

Su waye ministocin Tinubu? Jigon siyasa ya fadi dalilin jinkirin nada ministoci

The Cable ta rahoto Rewane yana cewa a ilmin tattalin arziki, abubuwa su na canzawa lokaci bayan lokaci, ya ce duk tsari akasin hakan ba ya aiki.

Yadda tattalin arziki zai farfado

A cewar masanin, gwamnatin tarayya ta na fuskantar kalubalen tashi da saukar farashin gangar mai, ya yi maganar karyewar darajar Naira.

Dole sai asusun kudin kasashen wajen Najeriya ya tashi kafin Naira ta farfado, Rewane ya kuma nuna bukatar kamfanonin ketare su shigo.

"Tashin Dala yana da hadari"

Da mu ka yi hira da shi, Dr. Usman Adamu Bello ya fada mana cewa hadarin tashin Dala ya fi na tsadar man fetur da ake kuka da shi yau a Najeriya.

A cewar masanin ko da an bude iyakoki domin shigo da abinci daga waje, kaya za su shigo da tsada domin Naira ba ta da darajar a zo-a gani a Duniya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel