Da Yawa Sata Su Ka Yi: Malamai 3,963 Ne Su Ka Fadi Jarabawar TRCN, an Fadi Wadanda Su Ka Yi Nasara

Da Yawa Sata Su Ka Yi: Malamai 3,963 Ne Su Ka Fadi Jarabawar TRCN, an Fadi Wadanda Su Ka Yi Nasara

  • Hukumar Kula da Jarabawar Malamai (TRCN) ta sanar da yawan malaman da su ka tsallake matakin
  • Magatakardar hukumar, Farfesa Josiah Ajiboye ya ce hukumar ta himmatu wurin tabbatar da kwarewar malamai a kasar baki daya
  • Ya ce daga cikin malamai fiye da dubu 15 da su ka rubuta jarabawar, fiye da dubu uku sun fadi jarabawar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Fiye da malamai dubu uku ne su ka gagara cin jarabawar da aka rubuta na hukumar TRCN.

Hukumar ta TRCN da ke kula da jarrabawar don gwajin kwarewar malamai ita ta bayyana haka a yau Litinin 18 ga watan Disamba, Legit ta tattaro.

Kara karanta wannan

An shiga jimamin rashin manoma 4 da 'yan bindiga suka yiwa kisan gilla a jihar Katsina

Malamai fiye da dubu uku ne su ka fadi jarabawar TRCN a Najeriya
Hukumar TRCN ta koka bayan malamai 3,963 sun fadi jarabawa. Hoto: Olukayode Jaiyeola/Pius Utomi Ekpei.
Asali: Facebook

Mene hukumar TRCN ke cewa kan jarabawar?

Magatakardar hukumar, Farfesa Josiah Ajiboye ya ce hukumar ta himmatu wurin tabbatar da kwarewar malamai don inganta ilmi a kasar baki daya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Punch ta tattaro Ajiboye na cewa:

"Akalla malamai 15,753 ne su ka rabuta jarabawar hukumar TRCN a cibiyoyi 38 a fadin kasar.
"Daga cikinsu, 10,636 wanda ke kunshe da kashi 72.9 cikin dari ne su ka tsallake yayin da 3,963 su ka fadi."

Mene dalilin faduwar mafi yawan malaman a jarabawar?

Farfesan ya ce wasu daga cikinsu ba su samu halartar jarabawar ba yayin da aka kashe sakamakon jarabawar wasu saboda satar amsa.

Rahotanni sun tabbatar da cewa an fara jarabawar ce a ranar 23 ga watan Nuwamba zuwa 25 ga watan Nuwambar da ta gabata, cewar Daily Post.

Hukumar TRCN ta saba yin jarabawar ga malamai musamman wadanda su ka kware ta fannin koyarwa don tabbatar da kwarewar tasu a kokarin inganta harkokin ilmi a kasar baki daya.

Kara karanta wannan

Gobara ta babbake ofisoshi akalla 17 a sakateriyar ƙaramar hukuma 1 a jihar Kano

JAMB ta kara kudin jarabawar UTME

A wani labarin, Hukumar JAMB ta bayyana karin kudin rijistar jarrabawar UTME a kasar zuwa fiye da naira dubu shida.

Wannan na zuwa ne yayin da ake cikin wani mawuyacin hali na matsin tattalin arziki a kasar.

A kwanakin baya ne hukumar ta fitar da sanarwar fara rijistar JAMB wanda ta saka a farkon sabuwar shekara da za mu shiga.

Asali: Legit.ng

Online view pixel