Dan Kano Mai Shekaru 26 da Ya Auri Ba’amurkiya Mai Shekaru 49 Ya Shiga Aikin Sojan Amurka

Dan Kano Mai Shekaru 26 da Ya Auri Ba’amurkiya Mai Shekaru 49 Ya Shiga Aikin Sojan Amurka

  • Matashi dan Najeriya mai shekaru 26 wanda ya fito daga jihar Kano kuma ya auri yar Amurka mai shekaru 49 ya shiga aikin sojan Amurka
  • Shekaru uku kenan da aka daura aurensu a masallacin Panshekara, jihar Kaduna
  • Kafin aurensu, Isah ya sha caccaka saboda banbancin shekaru, al'ada da addini tsakaninsa da Ba'amurkiyar

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Dan jihar Kano mai shekaru 26, Suleiman Isah, wanda ya auri Janine Reimann, Ba'amurkiya mai shekaru 49, ya shiga aikin sojan Amurka.

Kamar yadda jaridar Daily Nigerian ta rahoto, Isah ya auri Reimann a ranar 13 ga watan Disamba, 2020, lokacin yana da shekaru 23 ita kuma tana da shekaru 46.

Kara karanta wannan

"Zai shafe watanni 4:" Kotu ta tura wani matashi magarkama saboda satar doya a Abuja

Suleiman Isah ya zama sojan Amurka
Dan Kano Mai Shekaru 26 da Ya Auri Ba’amurkiya Mai Shekaru 49 Ya Shiga Aikin Sojan Amurka Hoto: Suleiman Isah
Asali: Facebook

An rahoto cewa soyayyar tasu ta sha suka da haifar da takaddama kama daga banbancin shekarunsu, al'ada da kuma addini.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ana tsaka da sukar, sai Isah ya auri Reimann a masallacin Panshekara, wanda ya samu halartan tsohon dan majalisa Sanata Shehu Sani.

A ranar Juma'a, 12 ga watan Mayu, Isah ya garzaya shafinsa na Facebook don sanar da babban labarin yana mai wallafa hotonsa sanye da rigar sojin Amurka.

Ya yi wa rubutun take da:

“Alhamdullillah- godiya ta har abada."

Sanata Shehu Sani ya kuma garzaya shafinsa na Facebook don taya ma'auratan murna kan matakin da Isah ya kai.

Ya ce:

"Sun caccake ni kan wannan aure na kabilanci, kuma yanzu Suleiman Isah ya yi aure cikin farin ciki kuma ya shiga cikin rundunar sojan California ta kasa. Ina taya shi murna."

Kara karanta wannan

Ba za ta yiwu ba: Sojoji sun fusata Pantami da hadimin Buhari da kisan masu Maulidi

Isah da Reiman sun hadu ne a Instagram, sannan suka shafe tsawon watanni goma suna tattaunawa kafin su sanar da aurensu.

Reiman, mai abinci mazauniyar Lindon, California, ta zo Najeriya don aure tsakaninta da Isah.

Budurwa na barar masoyi

A wani labari na daban, mun ji cewa wata matashiyar budurwa ta mika kokon baranta a gaban hadimin fitaccen mawakin Najeriya.

Cikin kuka budurwa ta roki Isreal da ya taimaka ya aureta. Kan haka ma ta ce ba sai ya biya kudin sadakinta ba domin shi take so ba kudinsa ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel