El-Rufai Ya Bar Mutane Cikin Duhu Da Ya Ziyarci Janar Babangida Bayan Haduwa da Buhari

El-Rufai Ya Bar Mutane Cikin Duhu Da Ya Ziyarci Janar Babangida Bayan Haduwa da Buhari

  • Nasir El-Rufai ya cigaba da wasu kai ziyara da yake yi tun bayan dawowarsa Najeriya daga kasar waje
  • Tsohon Gwamnan Kaduna ya je garin Minna saboda ya gaida Janar Ibrahim Badamasi Babangida a gidansa
  • Wasu mutane su na tunanin ziyarar ba za ta rasa burbushin siyasa ba, amma babu abin da yake nuna hakan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Niger – Malam Nasir El-Rufai ya sake shiga cikin labarai bayan ya kai wata ziyara wajen Ibrahim Badamasi Babangida.

Tsohon gwamnan na jihar Kaduna da wasu daga cikin mutanensa sun hadu da wajen Ibrahim Badamasi Babangida.

El-Rufai
Nasir El-Rufai da Ibrahim Babangida Hoto: MuyiwaAdekeye
Asali: Twitter

Nasir El-Rufai da Babangida (IBB)

Nasir El-Rufai ya ziyarci tsohon shugaban Najeriyan a gidansa a Minna a jihar Neja.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kara karanta wannan

Jerin mutane 8 da suka bada taimakon miliyan 700 da aka kashe masu Maulidi a Tudun Biri a Kaduna

Mai magana da yawun tsohon Ministan harkokin Abuja, Muyiwa Adekeye ya sanar da haka ranar Alhamis a shafinsa.

"Yau Malam Nasir El-Rufai yana Minna domin ziyartar tsohon shugaba na soja, Ibrahim Babangida."

- Muyiwa Adekeye

Da ganin hotuna suna yawo a Twitter, wasu su ka fara jefawa Muyiwa Adekeye tambayoyi a game da mai gidan na sa.

Malam Nasir El-Rufai ya je Daura, Kaduna

Ziyarar ta jawo magana ne ganin kwanan nan ne El-Rufai ya hadu da Muhammadu Buhari a gidansa da ke garin Daura.

Kafin zuwansa jihar Katsina, tsohon gwamnan Kaduna da Khalifa Muhammadu Sanusi II sun ziyarci garin Tudun Biri.

El-Rufai da Mai martaba Muhammadu Sanusi II sun yi wa mutanen kauyen ta’aziyyar mutanen da sojoji su ka kashe.

Ziyara ko shirin zaben 2027?

Watakila ziyarar Janar Babangida ba za ta rasa wuce ta zumunci ba, amma wasu suna ganin akwai wata manufa a kasa.

Kara karanta wannan

‘Yan Shi’a sun taso sojoji, sun nemi hukunta sojojin da suka kashe 'Yan Maulidi

Babangida wanda ya yi shekaru takwas ya na mulki tsakanin 1985 da 1993 ya na cikin manyan da ake ji da su a Najeriya.

Dawowar Nasir El-Rufai Najeriya

Ana da labari Nasir El-Rufai ya sanar da cewa kamfaninsu na Afri-Venture Capital Company Ltd zai fara aiki a Junairun 2024.

Daf da zai bar karagar mulki, El-Rufai ya soki manyan Arewa da tsarin canjin kudi da aka kawo a mulkin Muhammadu Buhari.

Asali: Legit.ng

Online view pixel