Sojoji Sun Karbi Shawarar Pantami da ‘Kuskure’ Ya Kashe Mutane Kusan 100 Ana Maulidi
- Hedikwatar tsaro ta bayyana cewa ta dauki darasi daga kuskuren da dakarun sojojin kasa a Tudun Biri
- Manjo Janar Edward Buba ya ce daga yanzu ba za a sake jefa bam ba sai an tabbatar da ‘yan ta’adda a wuri
- Maganar Janar Edward Buba ta zo daidai da wasu daga cikin shawarwarin da Isa Ali Pantami ya ba sojoji
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.
Kaduna - A sakamakon abin da sojoji su ka kira kuskuren da ya yi sanadiyyar rasa rayuka a jihar Kaduna, dole aka dauki wasu matakai.
Vanguard ta rahoto cewa daga yanzu kafin sojoji su saki bam, dole ne a tabbatar cewa ‘yan bindiga da ‘yan ta’adda za a hallaka a harin.
Masifar da ta aukawa mutanen Tudun Biri a ranar Lahadi ya jawo za a rika kaffa-kaffa bayan zanga-zanga da kuma suka da aka rika yi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Darektan harkar labarai a Hedikwatar tsaro a Najeriya, Manjo Janar Edward Buba ya bada tabbacin cewa za su kiyaye aukawa marasa laifi.
Janar Edward Buba ya ce kafin su harba bam a wuri, sai sun samu tabbaci dari bisa dari cewa ‘yan ta’adda ne abokan gaban da ake tunani.
"Daga yanzu za mu tabbata da abokan harinmu kafin mu saki bama-bamanmu.
A matsayin dakarun sojojin Najeriya, za mu cigaba da yin aikinmu tare da bin dokokin yaki, wanda a kullum mu ke la’akari da su a aikinmu.
A kan abin da ya faru a Kaduna, a ko yaushe sojoji su kan koyi darasi domin kiyaye gaba.
Sojoji za su yi hattara da kyau. Za mu tabbata ba mu sake samun irin haka nan gaba ba."
- Manjo Janar Edward Buba
DHQ: "Ba Arewa ake yaka ba"
A jawabin da ya yi, Janar Edward Buba ya yi watsi da zargin cewa mutanen Arewa ake yaka a boye, ya ce a gidan soja babu kabilar da babu.
Farfesa Isa Pantami ya ba sojoji shawara
An samu labari cewa tsohon Ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani ya ba sojoji shawarwari da su yi amfani wajen kare rayukan jama’a.
Farfesa Pantami ya ce akwai kayan aiki da ya kamata a tanada ta yadda za a guji taba marasa laifi sannan a horar da jami'an sojoji sosai.
Asali: Legit.ng